
Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya fara aiki a matsayin jakadan Nijeriya a ƙasar Ƙatar, inda ya samu gagarumar tarba daga jakadun ƙasashen Afrika 13 da manyan jami’ai a birnin Doha.
Farfesa Yakubu ya isa Doha a ranar Laraba, inda Daraktan Sashen Ladabi na Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙatar, Jakada Ibrahim Yousif Abdullah Fakhro, ya tarbe shi a filin jirgin sama cikin girmamawa.
Haka kuma, jakadun ƙasashen Afrikan, tare da Babban Sakataren Gas Exporting Countries Forum, Dakta Philip Mshelbila, da shugabannin al’ummar ‘yan Nijeriya mazauna Ƙatar sun yi masa maraba.
Sabon jakadan ya zo da gogewa mai yawa bayan shekaru goma yana jagorantar (INEC), wato daga 2015 zuwa 2025, inda ya jagoranci sauye-sauye masu muhimmanci a tsarin zaɓen Nijeriya tare da ƙarfafa amfani da fasaha da inganta sahihancin zaɓe.
Naɗin Mahmood Yakubu a matsayin jakadan Nijeriya a Ƙatar na nuna irin amincewar da gwamnatin tarayya ke da ita ga ƙwarewar da gogewarsa a harkokin shugabanci da difulomasiyya.
Ana sa ran zai taimaka wajen ƙara bunƙasa dangantaka tsakanin Nijeriya da Ƙatar a fannoni kamar kasuwanci, zuba jari, makamashi, ilimi da kuma hulɗar al’ummomin ƙasashen biyu.
Farfesan ya fara sabon babi a rayuwar aikin gwamnati, yayin da ake sa ran zai taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa alaƙar Nijeriya da Ƙatar a matakin ƙasa da ƙasa.
