
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Fafutukar kafa Ƙasar Biafara (IPOB), ta ce ta dakatar da Shugabanta, Nnamdi Kanu tare da tsige shi daga muƙamin daraktan Rediyo Biafara a matsayin wani ɓangare na sauya tsare-tsaren jagoranci da ayyukanta.
Shugaban kula da harkokin ƙungiyar, Chikadibia Edoziem ya sanar da haka a wata takarda, ranar Alhamis, bisa umarnin tawagar shugabancin ƙungiyar.
Edoziem ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne bayan wani taro da aka gudanar a ranar 17 ga Yuni, inda aka yi nazari kan wani rahoton sirri da ya shafi ganawar Kanu da jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) da Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa (NIA) a gidan yari.
Ƙungiyar ta ce matakin ya zama dole domin hana abin da ta kira kalamai marasa taka-tsantsan, tare da dakile amfani da sunan Nnamdi Kanu wajen aikata ayyukan da ka iya janyo tashin hankali ko rikici a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
Haka kuma bayyana cewa ba za ta ɗauki alhakin duk wani aiki da wasu mutane ko ƙungiyoyi marasa alaƙa da ita suka aikata da sunan Kanu ba.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da Nnamdi Kanu ke cigaba da zaman gidan yari bayan hukuncin ɗaurin rai da rai a watan Nuwamban 2025 da kotu ta yanke masa bisa samun sa da hannu a laifukan da suka shafi ta’addanci.
