
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya na duba yiwuwar gabatar da wani sabon shiri da zai ba ‘yan jarida damar raka jami’an tsaro yayin ƙaddamar da wasu atisaye a matsayin wani ɓangare na inganta lamuran tsaro a Nijeriya.
Za a yi haka ne da nufin bunƙasa fahimtar yanayin ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta ga ‘yan ƙasa da kuma tabbatar da tsare gaskiya da adalci akan harkokin sojoji.
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa ya bayyana a a ranar Alhamis yayin babban taron tsaron ƙasa da Ƙungiyar ‘Yan jaridar ta Ƙasa (NUJ) ta shirya a Abuja.
Ministan, wanda mai taimaka masa na musamman, Rear Admiral Olusanya Bankole ya wakilce shi, ya ce an tsara shirin ne domin ƙarfafa haɗin-gwiwa tsakanin gidajen jaridu da hukumomin tsaro da kuma inganta gaskiya da adalci a harkokin sojoji game da lamuran tsaro.
A cewarsa, fannin jarida shi ne muhimmin ginshiƙin wayar da kan al’umma akan ƙoƙarin jami’an tsaro, matakan gwamnati da ɗorewar al’amuran ƙasa musamman a lokacin da ake amfani da rikice-rikicen zamanin wajen gudanar da harkon yaɗa labarai da batutuwan al’umma.
Ya bayyana cewa, al’amarin gudanar da tsaro ba ga iya dakaru ya taƙaita ba, hatta ‘yan jarida suna da muhimmanci akan tsare-tsaren tsaron Nijeriya domin tabbatar ɗorewar lamuran ƙasa.
Kazalika, Janar Musa ya ce babbar manufar samar da shirin ita ce ba wa ‘yan jarida damar fahimtar ainihin abin da atisayen dakarun suka ƙunsa da kuma inganta ruwaito labaran tsaro yadda suka dace da daidai.
