Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kuma Jakadan Nijeriya da aka naɗa zuwa ƙasar Meziko, Mista Reno Omokri, ya bayyana muhimman fannoni da ake zuba kuɗaɗen da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan soshiyal midiya, Omokri ya ce matakin kawo ƙarshen tsarin tallafin man fetur ya bai wa Gwamnatin Tarayya damar karkata albarkatu zuwa ƙarfafa ajiyar kuɗaɗen musayar ƙasashen waje, ƙara rabon kuɗaɗe ga jihohi, tallafa wa hukumomin cigaban yankuna, bayar da lamunin karatu ga ɗalibai da kuma aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa a faɗin ƙasar nan.
A cewar sa, ɗaya daga cikin manyan nasarorin da aka samu shi ne ƙaruwar ajiyar kuɗaɗen musayar ƙasashen waje na Nijeriya. Ya ce wani rahoto na kamfanin JPMorgan Chase a watan Afrilu 2023 ya nuna cewa ajiyar kuɗaɗen musayar ƙasashen waje na Nijeriya ya kai kusan dala biliyan 3.7 jim kaɗan kafin gwamnatin tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta miƙa mulki ga gwamnatin Tinubu.
Omokri ya bayyana cewa tun daga lokacin, ajiyar kuɗaɗen ya haura dala biliyan 50, wanda ya ce zai taimaka wa ƙasar wajen fuskantar duk wata girgizar tattalin arziki a nan gaba, biyan kuɗin shigo da muhimman kayayyaki daga ƙasashen waje da kuma ƙara wa Nijeriya ƙima a idon masu ba da bashi da masu zuba jari.
Haka kuma ya yi nuni da ƙarin kuɗaɗen da jihohi suke samu ta hannun Kwamitin Raba Kuɗaɗen Tarayya (FAAC), inda ya ce rabon kuɗaɗen da ake yi a kowane wata ga matakan gwamnati uku ya ƙaru sosai tun bayan cire tallafin mai.
Da yake ambato alƙaluman watan Maris na shekarar 2022 da na Maris 2026, Omokri ya ce kuɗaɗen da FAAC ta raba sun tashi daga kusan naira biliyan 725.6 zuwa sama da naira tiriliyan 2, wanda hakan yana da nasaba da sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta kawo.
Omokri, wanda tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara ne, ya kuma yi magana kan kafa da kuma tallafa wa hukumomin cigaban yankuna a dukkan shiyyoyin siyasar ƙasar nan guda shida, yana mai cewa hukumomin da ke kula da Arewa-maso-Yamma, Arewa-ta-Tsakiya, Arewa-maso-Gabas, Kudu-maso-Yamma, Kudu-maso-Gabas da yankin Neja Delta suna samun gagarumin tallafin Gwamnatin Tarayya domin bunƙasa cigaban yankunan su.
A ɓangaren ilimi kuwa, Omokri ya ce sama da ɗalibai marasa galihu miliyan ɗaya na Nijeriya suna amfana da lamunin karatu ta hannun shirin Asusun Lamunin Ilimin Nijeriya (NELFUND). Ya ƙiyasta cewa an ware kusan naira biliyan 300 domin shirin a ƙarƙashin manufofin Shirin Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda).
Bugu da ƙari, sabon jakaden ya ambaci manyan ayyukan more rayuwa da ake ci gaba da aiwatarwa a matsayin hujjar yadda ake amfani da kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin mai. Daga cikin ayyukan akwai Titin Gaɓar Teku na Legas zuwa Kalaba, Babbar Hanyar Illela–Sakkwato–Badagiri da kuma Titin Trans-Sahara, waɗanda ya ce an tsara su ne domin inganta haɗin kai tsakanin shiyyoyin siyasar ƙasar nan.
Omokri ya yi nuni da cewa ƙarin kuɗaɗen da jihohi suke samu ya taimaka wa gwamnatocin jihohi da dama wajen biyan bashin albashi da kuma inganta ayyukan yi wa jama’a hidima.
Ya kuma ce jami’o’in Nijeriya sun samu kwanciyar hankali ta fuskar alaƙar ma’aikata da gwamnati fiye da yadda aka saba a ƙarƙashin gwamnati mai ci yanzu, yayin da ɗalibai suke da damar samun lamunin karatu ba tare da ruwa ba.
Jakadan da aka naɗa ɗin ya jaddada cewa amfanin cire tallafin mai yana bayyana a zahiri ta hanyar zuba jari a ayyukan more rayuwa, ilimi, cigaban yankuna da kuma tabbatar da daidaiton tattalin arziki.
Saboda haka ya yi watsi da iƙirarin da wasu suke yi cewa wai ‘yan Nijeriya ba su san inda kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin mai suka tafi ba, yana mai nuni da cewa ana mayar da kuɗaɗen ne zuwa shirye-shirye da ayyukan da aka tsara domin inganta walwalar al’umma da bunƙasa ci gaban ƙasa.
