Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi alƙawarin cewa Nijeriya za ta samar, ta watsa tare da rarraba aƙalla megawatt 10,000 na wutar lantarki cikin shekaru huɗu idan aka ba shi damar jagorantar ƙasar.
Obi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin podcast na Nevon Hƙ, wanda ɗan jarida kuma fitaccen mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Rufai Oseni, ke gabatarwa.
A yayin hirar, ya yi bayani kan matsalolin da ke addabar fannin wutar lantarki a Nijeriya da kuma hangen nesansa na yadda za a gyara lamarin.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce cimma samar da aƙalla megawatt 10,000 cikin shekaru huɗu abu ne mai yiyuwa, kuma hakan zai kawo gagarumin sauyi wajen samar da isasshiyar wutar lantarki ga al’umma da masana’antu.
“Idan aka ba mu dama, cikin shekaru huɗu za mu samar, mu watsa kuma mu rarraba aƙalla megawatt 10,000 na wutar lantarki,” inji Obi.
Sai dai lokacin da Rufai Oseni ya tambaye shi yadda zai aiwatar da wannan buri, Obi ya kauce wa bayyana cikakkun bayanai kan dabarunsa.
Yayin da yake mayar da martani, ya yi nuni da irin alkawurran da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi a baya, yana mai cewa ba lallai ne ɗan siyasa ya fito fili ya bayyana dukkan dabarunsa kafin ya hau mulki ba.
“Wani ya gaya muku cewa idan bai samar wa Nijeriya wutar lantarki ba kada ku zaɓe shi. Shin ya gaya muku yadda zai yi hakan? To me ya sa ni kuma dole ne na bayyana dukkan dabaruna a kasuwa?” inji shi.
Obi ya jaddada cewa ya kamata ’yan Nijeriya su fi mayar da hankali kan gaskiya da tarihin ayyukan wanda ke yin alkawari, maimakon matsa masa lamba ya bayyana dukkan tsare-tsarensa tun kafin ya samu damar aiwatarwa.
“Ba zan gaya muku yadda zan yi ba. Ba lallai ne ku san yadda zan yi ba. Abin da ya kamata ku yi shi ne ku duba mutumin da ke yin wannan alƙawari,” ya ƙara da cewa.
Nijeriya dai ta daɗe tana fama da matsalar ƙarancin samar da wutar lantarki duk da kasancewarta mafi girman tattalin arziki a nahiyar Afirka. Rashin isasshiyar wuta na ci gaba da zama ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke hana bunƙasar masana’antu, kasuwanci da ci gaban tattalin arziki.
Kalaman Obi sun sake tayar da muhawara kan yadda za a magance matsalar wutar lantarki a ƙasar, yayin da ’yan Nijeriya ke ci gaba da fatan samun shugabanci da zai kawo sauyi mai ɗorewa a wannan fanni.
