Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na kawo ƙarshen tsarin kiwo a fili a faɗin Nijeriya, a wani yunƙuri na zamanantar da harkar kiwo da kuma ƙara yawan amfanin da ake samu daga fannin.
Ministan Raya Dabbobi, Idi Maiha, ne ya bayyana hakan, inda ya ce gwamnati ta tantance filayen kiwo guda 470 da aka ware a hukumance, waɗanda za a gyara tare da mayar da su matsugunan makiyaya.
A cewarsa, wannan shiri zai taimaka wajen rage yawan zirga-zirgar shanu a manyan tituna da kuma cikin manyan birane kamar Abuja da Lagos.
Yayin da yake magana kan aiwatar da Tsarin Manufofin ƙasa na Samar da Madara, ministan ya ce mayar da makiyaya zuwa wuraren kiwo na dindindin zai sauƙaƙa wa gwamnati sa ido kan lafiyar dabbobi, inganta jinsunan kiwo da kuma ƙarfafa matakan daƙile cututtuka.
Ya bayyana cewa gwamnati na ƙarfafa makiyaya su rungumi tsarin zama a wuri guda maimakon yawo da dabbobi daga wannan yanki zuwa wani mai nisa.
Maiha ya ce idan makiyaya sun zauna a wuraren da aka tanada musu, zai fi sauƙi a aiwatar da shirye-shiryen tallafin gwamnati da nufin bunƙasa kiwon dabbobi da ƙara yawan amfanin da ake samu daga gare su.
Har ila yau, ministan ya bayyana cewa gwamnati na shirin ƙaddamar da tsarin sanya na’urorin bibiyar dabbobi ta hanyar fasahar lantarki.
A ƙarƙashin wannan tsari, za a riƙa saka alamar lantarki a jikin dabbobi domin gano su cikin sauƙi idan suka wuce iyakokin da aka ƙayyade, lamarin da zai taimaka wajen rage asarar dabbobi da kuma sace-sacen su.
Maiha ya jaddada cewa tsarin kiwo a fili na ƙara zama mai wahalar ɗorewa, yana mai cewa yawan tafiyar da shanu daga wuri zuwa wuri na rage yawan amfanin da ake samu daga su, tare da hana Nijeriya biyan buƙatunta na samar da madara.
Ya ce, yawan madarar da ake samarwa a Nijeriya har yanzu bai kai na wasu ƙasashen Afirka ba. A cewarsa, saniya a Nijeriya na samar da tsakanin lita 1.2 zuwa 2 na madara a rana, adadin da ya yi ƙasa idan aka kwatanta da wasu ƙasashe.
Ministan ya danganta ƙarancin samar da madara da matsalolin jinsunan dabbobi marasa inganci, rashin wadataccen abinci ga dabbobi da kuma raunin matakan kula da cututtuka.
Ya kuma bayyana cewa duk da cewa Nijeriya na da kusan dabbobi masu tauna ciyawa miliyan 270, ciki har da shanu, tumaki, awaki da raƙuma, har yanzu ƙasar ba ta samu babban ci gaba wajen inganta jinsunan dabbobi ba.
A cewarsa, ƙasashe da dama sun samu gagarumin ci gaba ta hanyar aiwatar da shirye-shiryen inganta jinsunan dabbobi cikin tsari, yayin da Nijeriya har yanzu ta fi dogaro da tsofaffin jinsunan shanu masu ƙarancin yawan amfanin kiwo.
