Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta umarci Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur ta ƙasa (NMDPRA) da ta ƙara tattaunawa da masu samar da iskar gas, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki domin ƙara yawan shigo da Gas ɗin Girki (LPG) cikin ƙasar nan, da nufin tabbatar da wadataccen kayayyaki tare da daidaita kasuwa a faɗin Nijeriya.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Aaramin Ministan Albarkatun Man Fetur mai kula da Gas, Ekperikpe Ekpo, ya fitar, wadda tashar talbijin na Channels ta samu a ranar Litinin.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun ministan, Louis Ibah, ya sanya wa hannu, ministan ya ce ya lura da damuwar da ‘yan Nijeriya ke nunawa kan tashin farashin gas ɗin girki a baya-bayan nan, tare da jaddada cewa Gwamnatin Tarayya na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da wadataccen, mai ɗorewa kuma mai sauƙin samu na iskar gas ga gidaje, masana’antu da kuma samar da wutar lantarki a ƙasar nan.
Sanarwar ta ce masu kasuwancin gas sun yi alƙawarin aara yawan gas ɗin da suke shigowa da shi daga ƙasashen waje domin cike giɓin da ake da shi tare da taimaka wa abin da ake samarwa a cikin gida.
Haka kuma, ministan ya bayyana cewa fara jigilar gas daga sabon cibiyar samar da gas ta kamfanin Seplat a watan Yuli zai taimaka matuƙa wajen ƙara wadatar gas a ƙasar nan.
Ekpo ya kuma tabbatar da cewa babu wani kamfani da ke fitar da gas ɗin da aka ware domin kasuwar cikin gida zuwa ƙasashen waje, yana mai cewa matakan sa ido da dokoki na ci gaba da aiki domin ba da fifiko ga buƙatun ‘yan Nijeriya.
Ya ce alamu sun nuna cewa wadatar gas ɗin girki a ƙasar nan za ta ci gaba da inganta, yana mai tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da za su ƙara samuwar gas, rage tsadarsa da kuma tabbatar da ɗorewar tsaron makamashi ga masu amfani da shi.
Ministan ya bayyana cewa tashin farashin gas ɗin girki da aka gani a baya-bayan nan ya samo asali ne daga matsalolin kasuwa da suka haɗa da sauyin darajar kuɗaɗen ƙasashen waje, tsadar sufuri, ƙarancin kayayyakin more rayuwa da kuma canje-canjen farashin LPG a kasuwannin duniya.
Ya ce bai kamata a ɗauki waɗannan matsaloli a matsayin gazawar manufofin gwamnati ba, domin kuwa gwamnati na ci gaba da aiwatar da matakan da za su daidaita kasuwar gas ɗin cikin gida.
A cewarsa, ɗaya daga cikin irin waɗannan matakai shi ne umarnin da aka bayar cewa duk gas ɗin girki da ake samarwa a Nijeriya ya kasance an ware shi ne domin biyan bukatun cikin gida kafin a yi tunanin fitar da shi waje.
“Wannan manufa ta taimaka wajen ƙarfafa wadatar gas a cikin gida, rage dogaro da shigo da shi daga ƙasashen waje da kuma ƙara ƙarfin kasuwar cikin gida wajen jure matsin lamba,” inji shi.
Wannan mataki ya biyo bayan wani rahoto da Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar, wanda ya nuna cewa matsakaicin farashin kilogram 5 na gas ɗin girki ya tashi daga Naira 7,655.73 a watan Maris zuwa Naira 8,706.93 a watan Afrilu.
Rahoton ya nuna cewa hakan ya kai ƙarin kashi 13.73 cikin ɗari idan aka kwatanta da watan Maris.
Haka kuma, NBS ta ce idan aka kwatanta da watan Afrilun shekarar 2025, matsakaicin farashin kilogram 5 na gas ya ƙaru da kashi 10.42 cikin ɗari.
Rahoton ya ƙara da cewa farashin cika tukunyar gas mai nauyin kilogram 12.5 ya tashi da kashi 13.89 cikin ɗari daga Naira 19,652.83 a watan Maris zuwa Naira 22,382.20 a watan Afrilu na shekarar 2026.
Kazalika, idan aka kwatanta da watan Afrilun shekarar 2025, farashin kilogram 12.5 na gas ya ƙaru da kashi 10.43 cikin ɗari daga Naira 20,268.06.
