Ƙungiyar wakilan ‘yan jaridu ta ƙaddamar da sabon ofishin ta bayan yi masa kwaskwarima a Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Ƙungiyar wakilan gidajen jaridu ta Jihar Kano, wato Correspondents’ Chapel, ta ƙaddamar da sabon ofishinta da aka yi wa cikakken gyara, a wani mataki na inganta yanayin aikin ’yan jarida da ƙara ƙarfafa haɗin kan mambobinta.

An gudanar da bikin ƙaddamar da ofishin ne a Sakatariyar Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Kano, ranar Lahadi, inda tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano kuma tsohon Shugaban NUJ na ƙasa, Muhammad Garba, ya jagoranci taron.

Manyan baƙin da suka halarci taron sun yaba wa Shugaban Correspondents’ Chapel na Kano, Murtala Adewale, da kwamitin gudanarwarsa, bisa ƙoƙarin da suka yi wajen inganta jin daɗin mambobi da samar da kyakkyawan wurin gudanar da ayyukan ƙungiyar.
Sun bayyana cewa gyaran ofishin wani muhimmin ci gaba ne da zai bai wa ’yan jarida damar gudanar da tarurruka, tattaunawa da masu ruwa da tsaki, da kuma gudanar da ayyukansu cikin yanayi mai kyau.

Da yake jawabi, Murtala Adewale ya ce an aiwatar da aikin ne domin samar da ingantaccen ofishi da zai zama cibiyar gudanar da ayyukan ƙwararru, horaswa da ƙarfafa haɗin kan mambobin ƙungiyar.

Ya kuma gode wa dukkan mutanen da suka bayar da gudunmawa wajen kammala aikin, yana mai cewa shugabancinsa zai ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da za su inganta jin daɗi da martabar ƙwararrun ’yan jarida a Jihar Kano.

By ukarofi

Leave a Reply