Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Shugaban asusun kula da Ilimi na gwamnatin jihar Nasarawa da ake kira NASETFund a turance Abubakar Adamu Idris ya samu digiri na uku a fannin jagoranci da ilimin harkokin ilimi daga jami’ar Atlantic International University.
Wannan ya zo ne bayan ya samu nasarar kare rubutunsa na digiri ɗin ƙarƙashin kulawar manyan malamai da aka san su a faɗin duniya.
A cikin wani bidiyo da aka fitar kwanan nan shugaban NASETFund din Abubakar Adamu Idris ya bayyana nasarar a matsayin sakamakon hakuri ta cikin ƙalubalen rayuwa da na karatu da kuma tsarin karatun digiri na jami’ar da ke da tsauri.
Da yake hira da ‘yan jaridar ciki har da wakilin mu game da wannan nasarar Adamu yace abin da ya ba shi kuzari shi ne sha’awar aikin sa da kuma burinsa na son samun mafi kyau a rayuwarsa.
Ya yaba wa gwamna jihar Injiniyan Abdullahi Sule inda yace salon jagorancinsa ne ya ba shi ƙwarin gwiwa ya kammala tafiyar karatun nasa.
Daganan sai Abubakar Adamu Idris wanda ke kuma riƙe da digiri na biyu a fannin harkoki da suka shafi Ilimi yayi amfani da damar inda yayi alƙawarin cigaba da jajircewa wajen tabbatar da sauyi na gari a fannin ilimin jihar da ƙasa baki ɗaya.
Wakilin mu ya kuma ruwaito cewa ita dai jami’ar Atlantic International University AIU din inda shugaban NASETFund din ya kammala karatun na musamman jami’a ce mai zaman kanta dake koyarwa ta nesa kuma tana da hedikwata ce a Honolulu dake ƙasar Hawaii.
