
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da aka sake kaɗa gangar siyasa a Nijeriya, wata tawagar Malaman Addinin Islama a Jihar Jigawa, ta bayyana goyon bayanta ga sake zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 da ke tafe.
A wani taro da aka gudanar a Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa, an manyan malamai daga jihohin Arewa goma 19 da adadinsu ya kai kusan 500, inda suka bayyana amincewarsu ga takarar Shugaba Tinubu.
Haka kuma, sun amince kan lallai shi za su yi wa yaƙin neman zaɓe kuma za su zaɓe a yayin zaɓukan, waɗanda za a gudanar a matakai daban-daban kama da na shugaban ƙasa, ‘yan majalisar dokokin ƙasa, gwamnoni da ‘yan majalisun dokokin jihohi.
Taron ya samun halartar wasu daga cikin gwamnonin jihohin Arewa, sai kuma Alhaji Kabiru Ibrahim Masari, Sanata Barau, Ministan Gine-gine; Muttaƙa Rabe Darma tare da wasu manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa.
Kazalika, an zaɓo malamai guda 12 daga kowacce jih daga mabambantan aƙidu ciki har da ɗariƙu, izala da tajdid. Har ila yau, an samu wakilcin limaman juma’a, mahaddata da malaman addini mata.
Malaman sun yi jawabi ne akan irin ayyukan alherin da Shugaba Tinubu ya samar wanda hakan ne ya sanya ya zama wajibi a garesu su goyi bayan takararsa a 2027, kamar yadda aka bayyana a wata takarda.


