Matasan malaman Zamfara sun yi addu’o’i ga Tinubu da Yari a matsayin shugaban kamfen na 2027

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Reshen Jihar Zamfara na ƙungiyar malamai matasa don wa’azi da faɗakarwa, (Zamfara United of Youth Scholars for Preaching and Guidance) yau Lahadi sun gudanar da zaman addu’o’i na musamman don samun nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nasarar Sanata Abdulaziz Abubakar Yari a matsayin darakta janar na majalisar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2027.

An gudanar da zaman addu’o’in, a zauren taro na Maryam Multi-Purpose Hall da ke Gusau, babban birnin jihar. Taron ya samu halartar malamai da ɗalibai daga faɗin jihar.

Da yake jawabi a wurin taron, shugaban ƙungiyar, Malam Naziru Ibrahim Buda, ya ce sama da ɗaliban Islamiyya 5,000 daga makarantun Islamiyya daban-daban a Gusau suka hallara don addu’o’in.

Ya yaba wa shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda zaɓar Sanata Yari a matsayin Shugaban kamfen na 2027, yana mai bayyana naɗin a matsayin abin da ya cancanta.

“Manufar zaman addu’ar ita ce a yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu addu’a don samun nasarar sa a Karo na biyu da kuma Sanata Abdulaziz Yari a matsayin babban daraktan yaƙin neman zaɓensa na 2027.” Ya ƙara da cewa

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa malaman matasa daga faɗin Jihar Zamfara sun halarci taron.

Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatocin jiha da na tarayya da su ƙara himma wajen inganta tsaro a jihar da kuma Arewa maso Yamma gaba ɗaya.

Malaman sun yi addu’ar zaman lafiya, haɗin kai, da kuma nasarar aiwatar da ajandar sabunta alƙiblar Nijeriya da shugaban ƙasa bola Ahmed Tinubu ya ayyana kafin babban zaɓen 2027.

By ukarofi

Leave a Reply