Tinubu ya sabunta wa’adin jagororin NAN da NTA

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya sabunta wa’adin Malam Ali Muhammed Ali, wato Darakta Manaja na Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), na tsawon wasu shekaru uku. Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ranar Lahadi.

Ya ce, shugaban ƙasar ya kuma sabunta na jagorancin Darakta Janar na Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA), Malam Abdulhamid Dembos. A cewar Onanuga, shugaban ya naɗa Dembos na NTA da Ali na NAN a ranar 20 ga watan Oktoba, 2023, inda ya ƙara da cewa, zangon nasu na biyu zai fara aiki ne a ranar 20 ga Oktoba, 2026.

Ya ƙara da cewa, Dembos, ɗan asalin Jihar Adamawa, shi ne tsohon shugaban Ƙungiyar Ma’aikatan Gidajen Yaɗa Labarai da na Harkokin Finafinai (RATTAWU), kuma a baya ya yi aiki a matsayin shugaban tallatawa na NTA bayan ya yi ritaya a 2017. Sannan, ya fara aiki ne da NTA a matsayin mai sanarwa a tashar Kaduna bayan kammala hidimar ƙasa a 1989.

A ɗaya gefen kuma, Kakakin ya ce Ali Muhammad Ali tsohon ɗan jarida kuma manajan harkokin yaɗa labarai ne mai ƙwarewa har na tsawon sama da shekara 30.

Ya yi digirinsa na farko a tsangayar Turanci a Jami’ar Bayero da ke Kano. Sannan yana da digiri a fannin Harkokin Ƙasa-da-ƙasa a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da kuma Difuloma a Tsangayar Koyon Aikin Jarida ta Jami’ar Bayero da ke Kano.

A ƙarshe, Onanuga ya ce shugaban ya kirayi jagororin biyu da su kasance masu ƙoƙarin sauke nauye-nauyen da aka ɗora musu bisa gaskiya da adalci da kuma nuna ƙwarewa kamar yadda ake kyautata zato gami da ciyar da Ajandar Sabunta Fata ta gwamnatin Tinubu gaba.

By Babaji

Leave a Reply