Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe
Ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen cike gurbin kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar Gombe/Kwami/Funakaye, Injiniya Dakta Usman Maijama’a Kallamu, ya yi kira ga sauran ’yan takarar da suka fafata da shi, shugabannin jam’iyya da magoya baya da su haɗa kai domin tabbatar da nasarar APC a zaɓen da za a gudanar ranar 19 ga Satumba, 2026.
Kallamu ya yi wannan kira ne bayan ya samu tikitin jam’iyyar a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a Malam Sidi, hedkwatar ƙaramar hukumar Kwami ta Jihar Gombe.
A zaɓen fidda gwannin, Kallamu ya samu ƙuri’u 27, inda ya doke sauran ’yan takarar da suka fafata da shi domin neman tikitin APC.
Da yake jawabin godiya bayan ayyana shi a matsayin ɗan takarar jam’iyyar, Kallamu ya yaba wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, shugabannin APC, wakilan zaɓe da magoya baya bisa goyon baya da amincewar da suka nuna masa.
Ya kuma yi kira ga sauran ’yan takarar da suka fafata da shi da su ajiye bambance-bambancen da suka biyo bayan zaɓen fidda gwani, su haɗa kai domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a babban zaɓen.
“Ina kira ga dukkan ’yan’uwanmu da suka fafata a zaɓen fidda gwani, shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki da magoya baya da mu manta da abin da ya faru, mu haɗa kai domin samun nasarar babbar jam’iyyarmu,” in ji shi.
Kallamu ya kuma nemi goyon bayan al’ummar ƙananan hukumomin Gombe, Kwami da Funakaye, yana mai alƙawarin bayar da wakilci nagari da kuma ƙoƙarin jawo ayyukan ci gaba ga al’ummar mazaɓar idan aka zaɓe shi.
Ya ce nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwani ba nasara ce ta mutum ɗaya ba, sai dai wata dama ce ta buɗe sabon shafi na haɗin kai da ƙarfafa APC domin tabbatar da samun wakilci mai inganci ga al’ummar mazaɓar.
Zaɓen cike gurbin ya biyo bayan rasuwar tsohon ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar, Hon. Yaya Bauchi Tongo, a watan Yunin 2026.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanya ranar Asabar, 19 ga Satumba, 2026, domin gudanar da zaɓen, wanda zai gudana a rumfunan zaɓe 903 da yankunan rajista 31 da ke ƙananan hukumomin Gombe, Kwami da Funakaye.
