
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da ake tsaka da lokacin damina, Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMet), ta yi hasashen samun hadari da tsawa a yankunan Nijeriya a ranar Litinin, 24 ga Agusta, 2026 tare da matsakaicin ruwan sama a sassa da dama na ƙasar.
Blueprint ta ruwaito cewa, hasashen ya ƙunshi shiyyoyin arewaci, arewa ta tsakiya da kudanci ƙasar, inda za a yi tsawa da matsakaicin ruwan sama a jihohi da dama a yinin. A jihohin arewa, NiMet ta ce ana sa ran hadari a safiya, yayin da tsawa za ta biyo baya tare da matsakaicin ruwan sama a rana da dare.
Ga jihohin arewa ta tsakiya, hukumar ta yi hasashen samun hadari a lokutan safiya tare da matsakaicin ruwan sama a sassa da dama na Abuja, Nasarawa, Benuwai, Kogi, Neja da kuma Filato a rana da kuma dare.
A jihohin kudanci kuwa, ana sa ran samun hadari da safe, da kuma yiwuwar ruwan sama a sassan jihohin Ibonyi, Inugu, Kuros-Riba da Akwa-Ibom. Ta yi hasashen samun matsakaicin ruwan sama a sassan shiyyar a rana da kuma dare.
Akan haka ne ta shawarci mazauna da su kasance masu kulawa da yanayin zirga-zirgarsu, tana mai gargaɗin yiwuwar samun guguwa gabanin tsawa. Haka kuma, hukumar ta shawarci hukumomin harkokin jiragen sama da su tabbatar da samun rahoton ba’asin yanayi daga gare ta domin taimaka wa shirye-shiryensu da kuma rage matakin aukuwar haɗari ga lamuran sufurin jiragen sama.
