Sojoji sun kama ƙasurgumin ɗan bindiga a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sojojin 17 Bridge sun sami nasarar kama ƙasurgumin ɗan bindiga Sunusi Mai Gilas a yayin da sojojin suka kai samame a ƙaramar hukumar Kurfi.

Mai gilas na ɗaya daga kwamandan ‘yan bindigan a dajin Danmusa wanda dama rundunar sojoji ke neman sa bisa zargin aikata ta’addanci da manyan laifuka a yankin na Ɗanmusa.

Wannan kame ya nuna nasarar da rundunar sojoji ke samu a ƙoƙarin da suke na tarwatsa sansanonin ‘yan bindiga da hana su kai wa da komowa a tsakankanin al’umma.

Yanzu jami’an tsaro sun fi mayar da hankali wajen gano wurare da dazuka da ake zargi da maɓoyar ‘yan bindigan a yankin.

Sojojin sun bayyana kamun Mai Gilas a matsayin wata dama na samu bayanan sirri kan duk wanni aikace aikacen ‘yan bindiga a yankin Ɗanmusa da Kurfi.

By ukarofi