Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano
Sheikh Kamalu Inuwa, Sarkin Malamai kuma Babban Limamin Masallacin Juma’a na Hidaya wanda ya ke unguwar Kwandila GRA, Gandun Albasa, a birnin Kano, ya bayyana cewa kyakkyawar mu’amala, wato ɗabi’a mai kyau ga al’umma, na daga cikin siffofin da Ubangiji ya sifanta Ma’aikin Allah (SAW) da su.
Ya ce haƙiƙa kyakkyawar ɗabi’a abu ne mai girma, saboda haka za a ga a koyarwar addini akwai Hadisai da ke nuna cewa kyakkyawar ɗabi’a tana daga cikin imani. Haka kuma, an bayyana a cikin addini cewa kyakkyawar mu’amala na iya kai mutum Aljanna.
Ya ce wannan lamari ne babba da ya kamata al’umma ta yi koyi da halayen Ma’aikin Allah (SAW) a kowane fanni na rayuwa, domin shi ne abin koyi da babu sama da shi, sai kuma ahalinsa, sahabbansa da sauran bayin Allah waɗanda suka biyo bayansu wajen kyautatawa.
Sarkin Malamai ya bayyana hakan ne a cikin huɗubarsa da ya gabatar a Juma’ar da ta gabata.
Haka kuma, ya ce kyakkyawar mu’amala ta haɗa da yaɗa sallama a tsakanin al’umma, zama lafiya da maƙwabta, sakin fuska ga jama’a da kuma kauce wa ɗaure fuska.
Ya ce daga cikin kyawawan ɗabi’u akwai tausayin ƙasa, girmama na gaba da kuma yi wa al’umma fatan alheri ba sharri ba.
Ya ce waɗannan kaɗan ne daga cikin kyakkyawar mu’amala da ake gani daga magabatanmu masu sada zumunci, inda ko da ba a ziyarce su ba, sukan ziyarci mutane, kuma idan sun je ba sa haɗa labarin sharri sai labarin alheri.
Ya ce sabanin wasu da ko wayarsu aka gani, ba a son a ɗaga domin ana tunanin labari mara daɗi ne za su faɗa.
Saboda haka, ya ce akwai buƙatar al’umma ta riƙa yaɗa labaran alheri, musamman kafafen yaɗa labarai kamar jaridu, rediyo, talabijin, kafafen sada zumunta da sauran hanyoyin sadarwa.
A ƙarshe, Sarkin Malamai, wanda kuma shi ne Babban Limamin Masallacin Juma’a na Hidaya, ya yi wa ’yan kafafen sada zumunta nasiha da su ji tsoron Allah, domin ya ce wasu abubuwan da suke yi a kafafen sada zumunta sun fi halayen dabbobi muni, duk da cewa mutum yana sane cewa shi Musulmi ne, ko ma ba Musulmi ba ne.
Ya ce babu wani addini da yake koyar da mummunan aiki ko alfasha.
Ya bayyana cewa abin takaici ne yadda wani mutum zai bar duniya amma bai kuɓuta daga sharrin wasu ’yan kafafen sada zumunta ba.
Saboda haka, ya buƙaci a sanya tsoron Allah a cikin dukkan al’amura, tare da yi wa al’umma da ƙasa addu’ar samun zaman lafiya, arziki da ci gaba a Nijeriya da duniya baki ɗaya.
