
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwalejin RMK College of Advanced and Remedial Studies da ke Tudun Wada a Jihar Kano, ta shirya jagorantar taron ƙasa-da-ƙasa a karon farko mai taken: “Multidisciplinary Approach for Attaining Sustainable Development”.
A wata sanarwa da hukumar gudanarwar kwalejin ta fitar mai ɗauke da sanya hannu Ɗahiru Muhammad Maihula, ta ce za a gudanar da taron ne na tsawon kwana uku daga Laraba, 25 ga Nuwamba zuwa 27 ga Nuwamba, 2026, wanda zai haɗa masana, masu bincike, ƙwararru, ‘yan kasuwa da masu fafutukar samar da ci-gaba daga fannoni daban-daban.
Taron zai mayar da hankali ne akan rawar da ilimi, ƙirƙira da haɗaka suke takawa wajen magance matsalolin da lamuran ci-gaba suke fuskanta da ƙarfafa wa lamuran samar da gobe mai kyau ga al’umma.
Daga muhimman ababen da za a tattauna akansu akwai amfani da fasahar zamani ta AI a harkar noma, ilimi, kimiyya da fasaha, daidaita lamuran muhalli, makamashi, inganta ayyukan dijital, kasuwanci, shugabanci na gari, kiwon lafiya, rafe talauci, damawa da ɓangarorin jinsi da inganta matasa.
Haka kuma, mahalarta za su yi ƙoƙarin samar da hanyoyin warware muhimman matsaloli a fannonin ilimi, noma, kiwon lafiya, kariyar muhalli da tattali da kuma ƙarfafa haɗaka tsakanin masana, gwamnati, masana’antu da yankuna.
