Fitaccen jarumin Nollywood, Pete Edochie ya rasu a shekara 79

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Daɗaɗɗen jarumin nan na finafinan Nijeriya kuma ɗan jarida, Cif Pete Edochie ya rasu yana da shekaru 79 a duniya bayan fama da rashin lafiyar da ya shafi cutar dajin mafitsara, lamarin da ya kawo ƙarshen ayyukansa na tsawon shekaru a harkar yaɗa labarai da masana’antar finafinai.

Edochie ya rasu ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare a ranar Laraba, 25 ga Nuwamba, 2026 a Jihar Enugun Nijeriya. An sanar da haka ne a wata takarda da ɗansa, Leo Pete Edochie ya fitar a madadin iyalan kuma ya wallafa a kafar Instagram a ranar.

Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin miji, uba, ɗanwa kuma ɗan gida, inda ta kuma ce ainihinsa ɗan ƙauyen Akamnato da ke Ƙaramar Hukumar Ifite Nteja ne ta Jihar Anambara. Ta bayyana cewa, marigayin ya rayu ne da matarsa Barista Misis Josephine Edochie, ‘ya’yansa da shaƙiƙansa da kuma ‘yan danginsu da dama. Sannan, ta ce za a sanar da lokacin jana’izarsa a halin da ya dace. Iyalan sun yi fatan Ubangiji ya jiƙan sa da rahama ya kuma ba su haƙurin juriyan rashinsa.

Cif Edochie ɗaya ne daga cikin fitattun jaruman Nijeriya da ake yaba wa ayyukansu, musamman ganin yadda ya yi fice wajen iya shiri da bakandamiyar muryarsa mai ɗaukar hankalin, wanda aka sani da yawan fitowa a matsayin basaraken gargajiya a finafinan Nijeriya.

Jarumin ya samu ɗaukaka ne daga matakin ƙasa zuwa ƙasa-da-ƙasa a lokacin da ya fito a matsayin Okonkwo a shirin kwaikwayon littafin Things Fall Apart na Chinua Achebe da tashar talabijin na NTA ta haska a shekarar 1987.

By Babaji

Leave a Reply