Daga AISHA ASAS
Duk da cewa foundation na taimaka wa mata wajen ɓoye kuraje, abin da wasu ba su sani ba shi ne, wasu nau’o’insa na iya taimaka wa wajen haifar da sababbin kuraje ko ƙara tsananta waɗanda suke akwai.
A shafinta na bayanan kula da lafiyar fata, ƙungiyar Likitocin Fatar Jiki ta Amurka, wato American Academy of Dermatology (AAD), ta bayyana cewa wasu kayan kwalliya na iya haifar da nau’in kurajen da ake kira acne cosmetica. Wannan na faruwa ne idan kayan kwalliya suka taimaka wajen toshe ramukan fata, lamarin da kan haifar da ƙananan kumbura, fararen kuraje ko wasu alamomin kuraje a fuska.
Abin lura shi ne, ba sai mace tana da tarihin kuraje ba kafin ta fuskanci wannan matsala. Wata da a da ba ta fama da kuraje za ta iya fara ganin suna bayyana bayan ta fara amfani da wani kayan kwalliya da bai dace da fatarta ba.
Haka kuma, alamomin ba lallai ne su bayyana a ranar da ta fara amfani da samfurin ba. A cewar AAD, kurajen da kayan kwalliya suke haifarwa na iya bayyana bayan kwanaki kaɗan, ko kuma bayan watanni. Wannan na iya sa mace ta kasa gane cewa foundation ɗin da take amfani da shi ne ke taimakawa wajen haifar da matsalar. Sai ta fara neman wasu hanyoyin magance kurajen, alhali tana ci gaba da shafa kayan kwalliyar da ke taimakawa wajen haifar da su.
Amma masana sun bayyana cewa mace mai kuraje ba lallai ne ta daina amfani da dukkan kayan kwalliya ba. Abin da ya kamata ta zaɓi kayan da suka dace da fatarta, sannan ta guji duk samfurin da ta lura yana ƙara mata kuraje.
AAD ta ba da shawarar cewa masu fata mai saurin samun kuraje su riƙa neman kalmomi irin su oil-free, ma’ana samfurin da ba shi da mai a tsarin da ake nufi da wannan lakabi, da non-comedogenic, wato samfurin da aka tsara domin rage yiwuwar toshe ramukan fata.
Sai dai ya kamata a fahimci cewa rubuta non-comedogenic a jikin samfurin ba yana nufin an tabbatar da cewa ba zai taɓa jawo kuraje ga kowa ba. Fatar mutane ta bambanta, kuma abin da ya yi wa wata mace ba tare da matsala ba, zai iya zama matsala ga wata.
