
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da kafa kwamiti domin binciken zarge-zargen cin zarafin da ya haɗa Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk da wata baturiya, yayin da ta kuma dakatar da dukkan wasu harkoki a hukumance da tafiye-tafiyen basaraken har zuwa lokacin kammala bincike.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adun jihar, Bala Salisu Zango ne ya sanar da haka a wata takarda, inda ya ce Gwamna Umar Dikko Raɗɗa ya bayyana rashin jin daɗinsa akan zarge-zargen.
A cewar sanarwar, gwamnan ya umarci kwamitin da ya gudanar da binciken al’amarin da bai wa gwamnatin shawara kan matakin da ya dace ta ɗauka a kai. Haka kuma, wani ɓangare na matakan da gwamnatin ta ɗauka ya haɗa da dakatar da sarkin daga shiga dukkan wasu harkokin masarauta da tafiye-tafiye har sai kwamitin ya gabatar da sakamakon bincikensa.
Saidai, duk da cewa sanarwar ba ta bayyana waɗanda aka naɗa acikin kwamitin ba ko bayyana wa’adin da aka ɗiba musu na aikin, gwamnatin ta tabbatar wa al’umma cewa za a yi adalci kan al’amarin. Ta ce, za a tabbatar da aiwatar da dukkan sakamako da shawarwarin da kwamitin zai bayar, abin da ke nuna ƙoƙarin gwamnatin na warware zarge-zargen da ɗaukar matakan da suka dace bisa sakamakon binciken.
Akan haka ne gwamnatin ta kuma kirayi al’umma da su kwantar da hankali tare da cigaba da kiyaye doka da oda da gudanar da harkokinsu yadda aka saba yayin da ake binciken.
