Daga JOHN D. WADA a Lafia
Shugaban ƙungiyar haɗin gwiwar masu haƙar ma’adinai na gargajiya da karami ta ƙasa (NASSMCS), Alhaji Abdullahi Dantansidi, ya yi kira na musamman ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya saka masu haƙar ma’adinai na gargajiya a cikin shirin Sabon Fata ta hanyar kafa wani shiri na musamman na ƙarfafa su da kare lafiyarsu.
Dantansidi wanda kuma shi ne shugaban kamfanin Dantansidi Group ya yi wannan kira a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, wadda aka bayar ga manema labarai a ƙaramar hukumar Keffi ta Jihar Nasarawa.
Ya ce kimanin mutane miliyan 1.6 ne ke hakar ma’adinai na gargajiya da karami kai tsaye a Najeriya, yayin da miliyoyin ‘yan uwansu ke dogaro da wannan sana’a don rayuwa.
A cewarsa, masu haƙar suna aiki a Zamfara, Neja, Nasarawa, Filato, Kaduna, Taraba, Bauchi da sauran jihohin da ake haƙo ma’adinai, amma ba tare da kayan aiki na zamani, kayan kariya, horo na fasaha, tallafin kuɗi mai sauƙi ko damar shiga kasuwannin ma’adinai na halal ba.
Ya ce wannan yanayi na fallasa su ga haɗarin lafiya, hatsari da talauci, duk da arzikin ma’adinai da ke cikin al’ummominsu.
Yayin da yake yaba wa Gwamnatin Tarayya kan ƙoƙarin da take yi na tsara harkar haƙar ma’adinai ta hanyar ƙungiyoyin haɗin gwiwa da aka yi wa rajista, Dantansidi ya ce dole ne gyare-gyaren su isa ga talakawan masu hakar ma’adinai da ke yankunan karkara.
Ya roki shugaban ƙasa Tinubu da ya kafa shirin sabon bege na ƙarfafa masu haƙar ma’adinai na gargajiya da kare lafiyarsu, wanda za a gina shi a kan shirye-shiryen da ma’aikatar raya ma’adinai ta tarayya ke da su a yanzu.
Ya lissafa muhimman ɓangarori shida na shirin: amincewa, rajista da ba da lasisi; kayan aiki na zamani da cibiyoyin hakar ma’adinai na haɗin gwiwa; horo kan tsaro da kariya; tallafin kuɗi mai sauƙi da bunƙasa ƙungiyoyin haɗin gwiwa; kasuwannin ma’adinai na adalci da sarrafa ma’adinai a cikin gida; da bunƙasa al’umma da jin daɗin iyali.
Dantansidi ya yi kira ga shugaban ƙasa da ya umarci ministan raya ma’adinai, Dr Dele Alake, da ya gana da wakilan ƙungiyoyin haɗin gwiwar masu haƙar ma’adinai na gargajiya a faɗin ƙasa, inda ya ba da shawarar a fara tattaunawar cikin kwanaki 90.
Ya kuma ba da shawarar a fara shirin gwaji a shiyyoyin siyasa shida na ƙasar, tare da bayyanannun manufofi na rajista, horo, samun kayan aiki, tsaron ma’adinai da inganta rayuwa.
Ya ce masu haƙar ma’adinai a shirye suke su tsara kansu, su cika ƙa’idojin da ake buƙata, su kuma yi aiki tare da hukumomin gwamnati.
“Ba sadaka muke nema ba, muna neman dama, kariya, amincewa da damar da ta dace don ba da gudummawa ga ci gaban ƙasa,” inji shi.
