Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau
An samu mummunan haɗarin mota a jiya Litinin, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum 15 tare da jikkata wasu mutum 20, a hanyar da ta tashi daga ƙaramar hukumar Gummi zuwa garin Talata Mafara.
Mamatan da suka rasa ransu dai na cikin masu zuwa ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen Gwamna Dauda Lawal, wanda aka gudanar a Talata Mafara.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin tsananin damuwa da alhini, kasancewar dukkanin waɗanda suka rasa ransu matasa ne.
Duk da cewa rahotannin farko sun bayyana cewa mutum 13 ne suka rasa ransu, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC), SPR Aliyu Isah, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa motar na ɗauke da mutum 50 a lokacin da haɗarin ya faru.
A cewarsa, mutum 15 ne suka rasa ransu a wurin, yayin da wasu mutum 20 suka samu raunuka daban-daban.
Hukumar ta yi kira ga mambobin jam’iyyun siyasa da su kiyaye tuƙin ganganci a lokacin yaƙin neman zaɓe a jihar, domin kaucewa afkuwar irin wannan mummunan lamari a gaba.
Waɗannan su ne sunayen wasu daga cikin waɗanda suka samu hatsarin mota daga Gummi zuwa Talata Mafara, Imrana Garba Falale, Lirwanu Ludda Falale, Ummaru Karama Falale, Na Iya Falale, Lirwanu Dan Juma Gamo Falale, Saidu Tasha Falale, Bala Gabu Falale, Aliyu Kwamas Maikosa, Bala Mai Shayi Maikosa, Mani Gurmu Maikosa, Iyaka mutum 3, Bayan Dutsi mutum 1 da Kuma Kukoki mutum 1.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tuni aka gudanar da jana’izar mamatan bisa addinin Musulunci a jiya Litinin din.
Hakazalika, Gwamnatin Jihar Zamfara ta ɗage taron gangamin yaƙin neman zaɓen Gwamna Dauda Lawal da za a yi yau Talata a ƙaramar hukumar Maru.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Muhammad Dantawasa, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Gusau yau Talata.
Gwamnatin Jihar ta miƙa sakon ta’aziyyar ta ga iyalai da masoyan mamatan, da kuma al’ummar Gummi da ƙaramar hukumar Gummi baki ɗaya, bisa wannan babban rashi da aka yi.
Al’ummar Jihar Zamfara na ci gaba da yin addu’ar Allah ya jiƙan mamatan, Ya ba iyalansu haƙurin jure wannan rashi, Ya kuma bai wa waɗanda suka ji rauni saurin warkewa.
