Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Majalisar Masarautar da haɗa da Katsina da Daura ta gudanar da taron sirri da masu riƙe da sarautun gargajiya don tattauna muhimman batutuwa.
Taron, wanda aka gudanar a Gidauniyar Jihar Katsina Conference Hall da ke Katsina, ya kasance ƙarƙashin jagorancin Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman.
Taron ya haɗa mambobin majalisar masu sarautun Gargajiya, waɗanda suka tattauna batutuwan da ake ganin suna da muhimmanci ga ci gaba, zaman lafiya da kwanciyar hankali a masarautun na Katsina da Daura.
Ko da yake ba a bayyana cikakkun bayanai na tattaunawar ga jama’a ba, an bayyana taron a matsayin wani muhimmin taro da ya haɗa shugabannin gargajiya na masarautar.
Taron na zuwa ne daidai lokacin da Masarautar Daura ta shiga ruɗani dangane zargin da wata mata mai yawon buɗe ido tayi zargin Sarkin Daura ya ci zarafin ta.
Ba a ga Sarkin Daura a wajen taron ba.
