Tinubu ya buƙaci Majalisar Dokokin Ƙasa ta amince wa rage kasafin 2026 zuwa N65.176trn daga N68.323trn

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta soke tare da sake aiwatar da Dokar Kasafi ta 2026 yayin da ake neman a rage ainihin adadin jimillar kuɗaɗen da za a kashe daga Naira tiriliyan 68.323 zuwa Naira tiriliyan 65.176 a matsayin wani ɓangare na sauya tsarin kasafin Gwamnatin Tarayya da neman hakan ya dace da wajibai da arziƙin da ake da su a ƙasa.

Tinubu ya aike wannan buƙata ne ta wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 20 ga Nuwamba, 2026, wadda Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ya karanta yayin zaman majalisar na yau Talata.

A cikin wasiƙar, shugaban ya bayyana cewa kwaskwarimar da yake so a yi na da nufin dacewa da kasafin 2026 da matakin arziƙin da Gwamnatin Tarayya take da shi, yayin ƙoƙarin inganta lamuran tsayar da gaskiya da adalci da kuma tabbatar da aiwatar da kasafin bisa inganci.

Ya ce, hakan zai taimaka wajen daidaita wasu kashe-kashe da ake samu daga ɓangaren NPCL a madadin ƙasar, warware matsalolin nauye-nauyen basussukan da ake shirin samarwa, samar da halin tabbacin zuba jari da samar da tsare-tsaren dawo da kuɗaɗe ga ma’aikatu, rassa da hukumomi (MDAs) da kuma wasu asusu na musamman.

A cewarsa, sauran hukunce-hukuncen da aka ƙara da na da nufin kammala muhimman ayyukan titina, bayar da kariya ga samar da kayan noma, rage tsadar samarwa, inganta lamuran gona, bunƙasa samun damar shiga kasuwanni da warware matsalolin rashin ruwa acikin al’ummar Nijeriya.

A ranar 31 ga Maris, 2026 ne dai Shugaban ƙasar ya buƙaci a ƙara Naira tiriliyan 9.81 daga ainihin ƙiyasin kasafin na farko, wanda ya kai jimillarsa zuwa Naira tiriliyan ₦68.323.

By Babaji