
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Tarayya a Kano, ta sanar da ɗage shari’ar da ke ƙalubalantar ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar NDC a babban zaɓen 2027 zuwa ranar 7 ga Disamba, biyo bayan ƙorafi daga ɓangaren masu ƙara na a ƙara musu lokaci domin su bayar da amsa a tsanake akan inkarin da jam’iyyar ta yi na neman kotun ta yi watsi da shari’ar.
Wannan mataki ya zo ne bayan zaman shari’ar da aka yi a ranar Litinin, inda lauyan NDC, Barista Magaji Mato, ya shaida wa ‘yan jarida cewa masu gabatar da ƙara ba su kai ga bayar da masa ba akan inkarin kuma an gabatar musu da abin da kotu ta nema a makon da ya gabata.
A cewarsa, jam’iyyar ta shigar da ƙorafin neman kotun ta soke ƙarar tun farkon gabatar da ita domin masu ƙarar ba su gabatar da wata hujja ba da ke tabbatar da iƙirarin nasu. Sannan, ya ce jam’iyyar ba ta yi inkarin neman ɗage sauraron ƙarar ba, lamarin da ya sa kotun ta ɗage zuwa 7 ga Disamba.
Lauyan ya bayyana cewa, shari’ar ba matsala ce ta kafin zaɓe ba saboda mutane ukun da suka bayyana a matsayin masu ƙara, ba ‘ya’yan jam’iyyar ba ne. Sannan, ya ce ko da ‘yan NDC ne, ba su shiga cikin zaɓen fidda gwanin ɗan takarar gwamnan jam’iyyar ba wanda kwamitin ayyukanta na ƙasa ya gudanar a ranar 29 ga Mayu, 2026.
