Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi ta sami nasarar kama wani mutum mai shekaru 30, Tapro Tareza, ɗan ƙauyen Changu, da ke Gwazawa a ƙarƙashin Gundumar Kanya, bisa zargin tono gawa a maƙabartar Machika, Ribah.
Kamen ya biyo bayan rahotannin da aka samu a baya na lalata kaburbura a maƙabartar. Sakamakon haka, ‘yan sanda, tare da haɗin gwiwar matasa masu kishin ƙasa na yankin, su ka sanya ido domin kama wanda ke aikata laifin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan sufurtandan ‘yan sanda Bashir Usman ya bayyana cewa ranar 10 ga Nuwamba, 2026, da misalin ƙarfe 7:15 na dare, jim kaɗan bayan binne wani mamaci, an kama wanda ake zargi yana tono kabarin. Nan take matasa masu sa ido suka kama shi, suka kuma sanar da yan sanda.
Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin da cire wasu abubuwa daga jikin mamatan ya amsa cewa ya dade cikin ayyukan lalata kaburbura da aka yi a baya a maƙabartar nan, ciki har da wani lamari da ya gabata inda aka ce ya cire ya tafi da likkafani na wani mamaci. Kakakin rundunar ya ƙara da da cewa yanzu haka dai ana cigaba da bincike don gano cikakken halin da ke tattare da lamarin, tare da tabbatar da cewa wanda ake zargi ya fuskanci matakin shari’a da ya dace.
Rundunar ‘yan sandan ta jihar Kebbi ta yaba da sa ido da haɗin kan al’umma, tare da gargaɗin jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu, a duk lokacin da wani abu ya faru su rinka kai rahoto ga hukumar tsaro da ke kusa da su.
