Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano
Daya daga cikin matasa ’yan kasuwa kuma shugaban kamfanin Yammusa da ke Kano, Alhaji Ashiru Yammusa, ya bayyana cewa addu’a da burinsu shi ne ganin Nijeriya, wadda ta samu ’yancin kai a shekarar 1960, ta zama ƙasa mafi tsaro da zaman lafiya tare da tarin arziki.
Ya ce burinsu shi ne ganin an samu ƙasa da za a rasa masu kwana da yunwa, a rage yawan matasa marasa aikin yi, a samu ingantaccen tsarin kiwon lafiya, bunƙasar noma da kiwo, ingantaccen tsarin sadarwa da zirga-zirga, da kuma tituna da hanyoyi masu kyau ba tare da ramuka ba.
Yammusa ya bayyana wannan fata ne yayin da Nijeriya ke shirin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai a watan Oktoba na shekarar 2026.
Haka kuma, ya nemi shugabanni da su sanya kishin al’umma da ƙasa a zukatansu, ta yadda za a samu ingantattun makarantu da ilimi, musamman a fannonin kimiyya da fasaha, kasuwanci, ilimi, aikin gona da sauran fannoni domin Nijeriya ta yi daidai da sauran ƙasashen duniya.
A ƙarshe, ya shawarci ’yan Nijeriya da su zama masu ƙwazo kamar yadda aka san mutanen da, waɗanda suka yi fice wajen zumunci, taimakon juna, sanin ya kamata da sauran kyawawan halaye.
Ya kuma buƙaci shugabanni da sauran al’umma da su sanya tsoron Ubangiji a cikin dukkan al’amuran rayuwa, musamman ganin yadda rayuwa ta yi tsada sakamakon tsadar makamashi irin su man fetur, gas da makamantansu.
Ya ce al’umma na buƙatar a samu sauƙin rayuwa a kowane fanni a Nijeriya.
