Sojojin Nijeriya sun lallasa Lakurawa a Kebbi, sun ƙwace makamai da boma-bomai

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Rundunar OPERATION FANSAN YAMMA ta daƙile wani hari da ake zargin mayaƙan ƙungiyar Lakurawa ne suka kai tare da ƙwace makaman harba roka, abubuwan fashewa da wasu kayayyaki yayin wani samame a jihar Kebbi.

Wani rahoton aiki da aka bai wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Abuja a ranar Litinin ya ce sojojin rukuni na 2 na runduna ta 8 ne suka gudanar da wannan farmaki.

Rahoton ya bayyana cewa, sojojin sun yi arangama da waɗanda ake zargin ‘yan ta’addan ne a yankin Dogon Daji da ke ƙaramar Hukumar Dandi ta Jihar Kebbi a ranar Lahadi yayin wani samamen kai hari.

A cewar rahoton, ‘yan ta’addan sun buɗe wa sojojin wuta, amma ƙarfin makaman rundunar ya fi nasu, lamarin da ya tilasta musu tserewa daga yankin.

“Bayan haka, sojojin sun bi sawun waɗanda suka tsere tare da gudanar da aikin bincike da share yankin.”

“Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bututun harba roka, rokoki, wasu na’urorin fashewa ƙirar gida (IEDs), babura guda biyu, caja da wasu kayayyakin amfanin ‘yan ta’addan suka bari yayin da suka tsere.”

Rahoton ya ce babu wani soja da ya rasa ransa ko ya jikkata a yayin kai wannan samame.

Ya ƙara da cewa farmaki na daga cikin ci gaba da hare-haren da rundunar ofureshan Fansan Yamma ke kai wa domin tarwatsa cibiyoyin ‘yan ta’adda da a yankin Arewa maso Yamma.

A cewar rahoton, hare-haren da rundunar ke ci gaba da kai wa sun rage miyagun laifuffuka da damar gudanar da ayyukansu tare da lalata hanyoyin samar musu da kayan aiki da tallafi.

Rahoton ya kuma bayyana cewa sojojin na ci gaba da matsa lamba kan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda a faɗin yankin a yayin da ake ci gaba da da kai sabbin farmaki domin cafke waɗanda suka tsere da ƙarfafa nasarorin da aka samu.

By ukarofi

Leave a Reply