Ku daina ba ‘yan ta’adda satar amsa – Ministan Labarai ga gidajen jaridun Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan Al’umma, Mohammed Idris ya yi kira ga gidajen jaridun Nijeriya da su daina buɗe sirri ga ‘yan ta’adda da wasu ɓarayi, yana mai cewa cigaba da yawaita yaɗa ayyukansu dama ce ga masu son watsa fargaba da rashin zaman lafiya acikin al’umma.

Mohammed Idris ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin babban taro akan tsaro da Ƙungiyar ‘Yan jarida ta Ƙasa (NUJ) ta shirya da haɗin-gwiwar Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS), inda ya ce wajibi ne ‘yan jarida su samar da daidaito akan ‘yancin yaɗa labarai sakamakon nauyin ƙasa da ke kansu don ciyar da ita gaba.

“Da’alla ku ɗauke waɗannan ‘yan ta’addan da ɓarayin daga shafukan jaridunku na farko. Wannan shi ne abin da suke so”, inji Ministan.

Ministan yaɗa labaran ya koka da yadda rahotannin gidajen jaridu ke ƙara ɗaukaka sunan ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane yayin da ba a bayar da muhimmancin da ya dace ga ƙoƙarin hukumomin tsaro da ke aiki tuƙuru wajen ba rayuka da dukiyoyin al’umma tsaro.

A cewarsa, aikin jarida na haƙiƙa ba ya taƙaice labarai da wani ɓangare, saidai yana buƙatar ƙwararru a fannin su tabbatar da yin adalci wajen abin da ya kamata a ruwaito ko wallafa da yadda ya dace a gabatar da shi.

Ya ƙara da cewa, ‘yan jaridar da suka yi fice sune waɗanda suka san abin bai dace ba a ruwaito don masalahar gina ƙasa da ci-gabanta.

Kazalika, ministan ya ce Nijeriya na fuskantar ƙalubalen tsaro mai wahalar fahimta, ciki har da ta’addanci, bala’in masu tsatstsauran ra’ayi, laifukan yanar gizo, yaɗa labaran bogi, da shiryayyun miyagun laifuka, lamarin da ya sa haɗakar hukumomin tsaro da gidajen jarida ke da gagarumar muhimmanci.

Har ila yau, ya bayyana cewa ɓangarorin biyu na da muhimman rawa da za su taka wajen gina ƙasa, inda a lokacin da nauyin kare rayuka da dukiyoyi ke kan hukumomin tsaro, su kuma gidajen jarida su ke da alhakin zama idon al’umma da kuma tsani tsakaninsu da gwamnati.

By Babaji

Leave a Reply