Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta buƙaci ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Turai (UEFA) da ta sake buɗe matakan ladabtarwa kan abokiyar hamayyarta ta Barcelona, tana mai cewa ta samu wasu sabbin hujjoji da ke ƙarfafa zargin da aka daɗe ana yi wa ƙungiyar dangane da biyan kuɗaɗe ga wasu jami’an alƙalanci a abin da aka fi sani da shari’ar “Negreira.”
A cikin wata wasiƙa da ta aikewa UEFA, Real Madrid ta ce sabbin bayanan da take da su na ƙara ƙarfafa zargin cewa Barcelona ta riƙa biyan kuɗaɗe ga Jose Maraa Enriƙuez Negreira, tsohon mataimakin shugaban Kwamitin Fasaha na Alƙalan Wasa na Sifaniya, ta hanyar wasu kamfanoni da ke da alaƙa da shi.
Matakin na Real Madrid ya sake ƙara zafi a ɗaya daga cikin manyan rikice-rikicen shari’a da suka taɓa girgiza ƙwallon ƙafar Sifaniya, inda ƙungiyar ke ganin wajibi ne hukumomin ƙwallon ƙafa su ɗauki mataki domin kare mutuncin wasan yayin da ake ci gaba da gudanar da binciken laifi a Sifaniya.
A cikin wasiƙar da ta aika wa UEFA, Real Madrid ta bayyana cewa hujjojin da ta samu na nuna yiwuwar Barcelona ta shafe shekaru tana biyan kuɗaɗe ga kamfanonin da ke da alaƙa da Negreira ba tare da wani cikakken bayani ko hujjar da za ta tabbatar da dalilin biyan kuɗin ba.
ƙungiyar ta ce irin wannan tsari na iya haifar da shakku kan yiwuwar yin tasiri a kan hukuncin alƙalan wasa, lamarin da ke barazana ga adalci da gaskiya a gasa.
Real Madrid ta jaddada cewa dole ne a kare muhimman ginshiƙan wasan ƙwallo kamar tsaka-tsaki, daidaito tsakanin masu fafatawa da kuma rashin tabbacin sakamakon wasa.
A cewarta, duk wani tsari da zai iya yin tasiri a kan alƙalan wasa na lalata amincewar jama’a da kuma mutuncin gasa a matakin cikin gida da na Turai.
Real Madrid ta kuma bukaci UEFA da ta gaggauta sake buɗe shari’ar ladabtarwa da ta taɓa fara gudanarwa kan lamarin, tana mai cewa jinkirin da aka samu ba abin karɓa ba ne.
ƙungiyar ta ce UEFA na da alhakin kare gaskiya da mutuncin ƙwallon ƙafa a Turai, ko da kuwa har yanzu ana ci gaba da gudanar da binciken shari’a a Sifaniya.
A cewar wasiƙar, ya kamata UEFA ta yi amfani da ikon da take da shi na ladabtarwa domin ɗaukar matakan da suka dace wajen kare martabar wasan.
Real Madrid ta bayyana cewa wannan buƙata ba ta nufin tsoma baki cikin aikin kotuna ba ne, sai dai tabbatar da cewa hukumomin wasanni sun sauke nauyin da ya rataya a kansu.
Haka kuma, ƙungiyar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kasancewa cikin shari’ar da ake yi a Sifaniya a matsayin mai shigar da ƙara mai zaman kansa tare da amfani da duk hanyoyin doka da suke a buɗe.
Shari’ar “Negreira” ta samo asali ne daga binciken da ake yi kan wasu kuɗaɗe da rahotanni suka ce sun haura Euro miliyan 7.3, waɗanda ake zargin Barcelona ta biya tsakanin shekarun 2001 zuwa 2018 ga kamfanonin da Jose Maria Enriƙuez Negreira ke mallaka a lokacin da yake babban jami’in alƙalanci.
Sai dai Barcelona ta sha musanta duk wani zargin cin hanci ko rashawa, tana mai cewa kuɗaɗen da aka biya sun shafi rahotannin fasaha, ayyukan bibiyar ’yan wasa da kuma shawarwari kan alƙalancin wasa.
ƙungiyar ta dage cewa ba ta taɓa yunƙurin yin tasiri ga alƙalai ko neman wata fa’ida ta rashin adalci a wasanni ba.
