Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta musanta rufe mashigar Hormuz

Spread the love

Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar Iran ta bayyana cewa babu wani sahihin tushe da ke tabbatar da rahotannin da ke cewa an sake rufe Mashigin Hormuz, daya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar mai da kayayyaki a duniya.

Mai magana da yawun ma’aikatar, Esmail Baghaei, ya ce rahotannin da ke yawo kan batun ba su da inganci.

Wannan na zuwa ne bayan wasu kafafen yada labarai sun rawaito cewa rundunar IRGC ta sanar da rufe mashigin saboda takaddama da Isra’ila.

A cewar yarjejeniyar fahimtar juna da Amurka da Iran suka rattaba wa hannu a wannan mako, an amince a c gaba da bude mashigin ba tare da karbar kudin fito ba na tsawon kwanaki 60, yayin da ake tattaunawa kan makomar tsarin zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin tsakanin ƙasashen da al’amarin ya shafa.

By Babaji

Leave a Reply