Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya na ƙoƙarin haɗa kai da sarakuna domin domin ɗabbaƙa zaman lafiya da tsaro da haɗin kan ƙasa da cigaba mai ɗorewa a faɗin Nijeriya.
A yayin da yake wakiltarsa a yayin zaman kwamitin majalisar sarakuna (NTRC) karo na 8 a Dutsen jihar Jigawa a ranar Litinin, ministan yaɗa labarai da wayar da kan al’umma Mohammed Idris, ya miƙa saƙon shugaban ƙasa ga sarakunan da suka haɗu daga yankin Arewa.
“Gwamnatin Shugaba Tinubu tana sane da irin rawar da kuke takawa kuma a shirye take ta haɗa kai da sarakuna wajen samar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa da cigaba” inji ministan.
Idris ya yaba wa majalisar sarakunan na ƙarƙashin mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar, kan irin gudunmowar da yake bayarwa wajen samar da zaman lafiya da haɗin kai da tsaro da ci gaba.
A yayin da yake magana game da taken zaman majalisar na bana, “Zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a Arewa,” ya jaddada muhimmancin zaman lafiya a matsayin ginshiƙi na cigaba.
“Idan babu zaman lafiya ba za a samu cigaba ba, idan babu haɗin kai ba, ba za a samu cigaba mai ɗorewa ba. lallai ne mu duka mu ɗau hakan a matsayin nauyin da ke kanmu,” ya faɗa.
Ministan ya bayyana sarakuna da zama muhimman abokan haɗin guiwa wajen shgabanci da samar da zaman lafiya saboda irin kusancinsu da al’umma da kuma iya tattaunawa da su game da manufofin ƙasa.
“Na tsawon ƙarni, sarakuna su ne ginshiƙin kiyaye al’ada da tsari da shiga tsakani a lokacin tashe-tashen hankula da zama kada tsakanin gwamnati da al’umma. Irin tasirin kusancinku da al’umma ya sa kuka zama muhimman abokan tafi da gwamnati da samar da zaman lafiya da motsa al’umma,” ya jaddada.
A game da tsaro, ministan ya ce, gwamnatin shugaba Tinubu ta ƙara ƙarfafa tsari a rundunar sojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro wanda ya sa aka cimma nasarori kan ƙungiyoyin ta’addanci.
Sai dai ya ce, sojoji kaɗai ba za su iya tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa ba.
“Lallai ne mu magance talauci da rashin aikin yi da wariya da kuma ƙarancin damarmaki na bunƙasa tattalin arziƙi waɗanda ke haddasa matsalar tsaro,” ya faɗa.
Ministan ya haska irin shirye-shirye da gwamnatin ke yi da suka shafi noma da kiwo da ma’adanai da samar da ayyuka da ɗaukar nauyin ilimi da bashin sayen kayayyakin amfanin yau da kullum da tallafa wa masu ƙananan sana’o’i.
Ya kuma bayyana samar da ma’aikatar bunƙasa kiwo a matsayin babban cigaba da zai zamanantar da harkar kiwo da rage tashe-tashen hankula da samar da ayyukan yi.
Haka kuma ya ce akwai manyan ayyukan tituna 4 da za su zama abin tunawa — titin Legas zuwa Calabar da titin Sokoto-Badagry da titin Calabar-Abuja da titin Akwanga-Jos-Bauchi-Gombe — waɗanda za su haɗa garuruwa da ba da damar faɗaɗa kasuwa da samar da ayyukan yi da zuba jari ga ƙasa.
Ya ƙara da cewa shirin sabunta fatan ‘yan Nijeriya na ƙokarin samar da damarmaki ta hanyar shiri kamar na NELFUND da CREDICORP da tallafa wa masu ƙananun sana’o’i da matsakaita a yayin da ya buƙaci sarakunan gargajiya da taimaka wajen yaƙi da labaran ƙarya da ɗabbaƙa kishin ƙasa.
Ministan ya nuna ƙarfin guiwarsa cewa taron zai samar da shawarwari na zaman lafiya da ci gaba. Ya kuma miƙa ta’aziyyarsa kan rasuwar manjo-janar, Rabe Abubakar.
“Muna miƙa ta’aziyyar ɗan kishin ƙasa…Rasuwarsa ta yi mana zafi sosai wanda ke tuna mana buƙatar ci gaba da dagewa wajen magance matsalar tsaro.
