Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sake jaddada cewa jihar na ci gaba da samar da yanayi mai kyau ga harkokin kasuwanci da zuba jari, ta hanyar daidaita manufofinta da ajandar sauye-sauyen Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnan ya ce, tsawon shekaru jihar ta aiwatar da wasu muhimman gyare-gyare da suka haɗa da ƙara gaskiya a harkokin gwamnati, ƙarfafa cibiyoyi, sauƙaƙa hanyoyin gudanarwa, ƙarfafa zuba jari da kuma inganta ayyukan hidima ga jama’a.
Uba Sani ya bayyana hakan ne a zaman fasaha na taron Majalisar Shugaban ƙasa Kan Samar da Sauƙin Gudanar da Kasuwanci (PEBEC) da rangadin jihohi, wanda aka gudanar a Kaduna ranar Alhamis.
Da yake jawabi ta bakin Kwamishinar Kasuwanci, ƙirƙire-ƙirƙire da Fasaha, Hajiya Patience Fakai, gwamnan ya ce sauye-sauyen da aka aiwatar sun fara haifar da sakamako mai kyau.
Ya ce, “A sabon rahoton tantance sauƙin gudanar da kasuwanci a matakin jihohi, an sanya Jihar Kaduna a matsayi na biyu mafi kyau a Nijeriya. Duk da cewa muna alfahari da wannan nasara, mun san cewa gyara da ci gaba tafiya ce mai ɗorewa ba wai wani mataki ne da za a ce an kai ƙarshe ba.”
Gwamnan ya nuna fata cewa taron fasahar na wannan rana zai ba da damar ƙara fahimta kan muhimman fannoni na gyare-gyare, ciki har da tantance tasirin dokoki, kula da ƙwarewar masu zuba jari, daidaita haraji da kuɗaɗen gwamnati, warware rikice-rikicen kasuwanci, sauye-sauyen fasahar zamani da kuma ma’aunan da ke ƙarfafa gasa tsakanin jihohi.
A cewarsa, Jihar Kaduna na farin cikin ganin cewa wannan taro ya samar da dandali na koyo, musayar ƙwarewa da kuma haɗin gwiwa wajen nemo mafita ga matsaloli.
Ya ƙara da cewa, “Darussa da shawarwarin da za su fito daga wannan taro za su ƙarfafa aiwatar da gyare-gyarenmu tare da taimaka mana wajen ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan wuraren da masu zuba jari ke son zuwa a Nijeriya.”
Gwamna Uba Sani ya kuma ƙarfafa mahalarta taron da su shiga tattaunawa sosai, su bayyana ƙwarewarsu cikin buɗaɗɗen zuciya, tare da amfani da ilimin da tawagar PEBEC ta kawo Kaduna.
A nata jawabin, Darakta Janar ta PEBEC, Gimbiya Zahrah Mustapha Audu, ta ce wannan taro ya yi daidai da muhimmin ginshiƙi na Ajandar Sabuwar Fata ta Shugaba Tinubu.
Ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi imanin cewa sauyin tattalin arziki mai ɗorewa ba zai samu ba sai idan gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi sun yi aiki tare cikin haɗin kai.
Ta ce, “Makomar tattalin arzikin Nijeriya ba za a tantance ta a Abuja kaɗai ba. Za a tantance ta ne a jihohi irin su Kaduna, ta hanyar ƙarfin tattalin arzikinsu na cikin gida, gasa tsakanin kasuwanci, ingancin ababen more rayuwa, tasirin cibiyoyi da kuma amincewar masu zuba jari da damar da suke gani a gabansu.”
Zahrah ta bayyana cewa Jihar Kaduna na da manyan fa’idodi na gasa saboda matsayinta na ƙofar shiga Arewacin Nijeriya, hanyoyin sufuri masu faɗi da kuma bunƙasar harkokin noma.
Ta kuma ce bunƙasar masana’antu, ƙarfafan cibiyoyin ilimi, wadataccen jarin ɗan Adam da kuma damarmaki a fannoni kamar masana’antu, sufuri da rarrabawa, fasaha, makamashi mai sabuntawa da kasuwancin noma sun sanya Kaduna cikin jihohin da suka fi jan hankalin masu zuba jari a Nijeriya.
A cewarta, kusancin jihar da manyan kasuwanni, haɗin hanyoyin jirgin ƙasa da tituna, yankunan masana’antu da kuma jajircewarta wajen aiwatar da gyare-gyaren kasuwanci sun samar da tubali mai ƙarfi ga bunƙasar tattalin arziki da jawo hankalin masu zuba jari.
Sai dai ta yi nuni da cewa ƙalubalen ba rashin damarmaki ba ne, illa yadda za a tsara su da kyau, a tallata su yadda ya kamata, tare da samar da yanayi mai kyau da zai ƙara wa masu zuba jari ƙwarin gwiwa.
Ta shawarci Jihar Kaduna da ta ci gaba da ƙarfafa fannoni da take da fifiko a cikinsu, ta zurfafa gyare-gyaren da ke sauƙaƙa gudanar da kasuwanci, ta inganta ababen more rayuwa da kuma tallafa wa ci gaban kamfanoni masu zaman kansu.
