Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ADC na jihar Kebbi Alhaji Musa Muhammad Dagwaya ya nemi haɗin kan ‘ya’yan jam’iyyar ADC na jihar da ba su sami nasarar a tsayar da su takarar kujerar muƙaman siyasa ba.
Ya yi wannan kira ne a wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ADC na gundumar Kebbi ta Arewa ranar Talatar da ta gabata a garin Argungu.
Alhaji Musa Dagwaya ya bayyana cewa a matsayin mu na Musulmi duk mun san duk abinda ya faru to daman rubutacce ne saboda Allah ya riga ya gama tsara komai tun farkon duniya saboda haka yana da kyau Musulmi ya kasance mai ɗaukar ƙaddara mai kyau ko kuma akasin haka.
Yanzu abin da ya rage shi ne kowa ya zo a haɗa hannu a gudu tare a tsira tare.
Ya kuma bayar da tabbacin jam’iyyar ADC a shirye ta ke da ta yi wa kowa adalci. Ta san irin gudummawar da kowa ke iya bayarwa saboda haka kowa ya bayar ta sa gudummawar domin tinkarar zaɓe mai zuwa.
Ya ƙara da cewa yanzu jam’iyyar ADC tana buƙatar sadaukarwa ne domin tinkarar gwamnati wanda kowa ya sani ba abu ne mai sauƙi ba, a zo a haɗa hannu tare domin samun nasara duk da ya ke a kullum jam’iyyar ADC tana ƙara samun karɓuwa daga ko ina faɗin ƙasar nan.
Ya kuma yi kira ga sauran shugabanni daga sassa daban-daban da kowa ya koma mazaɓar sa ya cigaba da wayar da kan mutane da su yi ƙoƙari su karɓi katin jifar ƙuri’a.
