Sojoji sun tono gawar fitaccen jagoran ‘yan bindiga, Kachalla don gudanar da bincike a Jihar Kogi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Rundunar Sojin Nijeriya ta tono gawar wani fitaccen jagoran ‘yan bindiga da ake zargi, Ibrahim Battijo wanda aka fi sani da Kachalla, daga wani daji a Jihar Kogi domin gudanar da binciken kimiyyar laifuka (forensic eɗamination) da kuma gwajin gano musabbabin mutuwarsa (autopsy).

Aikin ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Kwamandan Brigade ta 12 da ke Lokoja, Brigadier General Karim Sidi, wanda ya jagoranci tawagar sojoji zuwa wani daji da ke kusa da Iluke a gundumar Bunu, ƙaramar Hukumar Kabba/Bunu, a ranar Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da aikin ne domin tabbatar da cikakkun bayanai game da yadda Battijo ya mutu tare da tallafa wa binciken da ake yi kan lamarin.

An ce an kashe Battijo ne a ranar 10 ga Yunin 2026 lokacin da shi da wasu ‘yan bindiga suka yi yunƙurin sace ɗaliban da ke rubuta jarabawar kammala sakandare ta WAEC (WASSCE) a garin Iluke, amma suka gamu da turjiya daga jami’an tsaro.

Masani kan harkokin tsaro da yaƙi da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana cewa tono gawar ya zama dole domin ci gaba da bincike da kuma tattara hujjoji kan yadda aka kashe wanda ake zargin shugaban ƙungiyar ‘yan bindigar.

A cewarsa, rundunar sojin ta shiga cikin dajin inda aka binne gawar bayan artabun da ya kai ga mutuwarsa.

Makama ya ce: “Tawagar da Kwamandan Brigade ta 12, Brigadier General Karim Sidi, ya jagoranta ta shiga dajin da ke kusa da Iluke a yankin Bunu na karamar hukumar Kabba/Bunu domin tono gawar fitaccen shugaban ‘yan bindiga Ibrahim Battijo domin gudanar da binciken autopsy.”

Ya ƙara da cewa an hallaka Battijo ne yayin da yake kokarin jagorantar wani babban farmakin sace ɗaliban WAEC a yankin.

Wannan ci gaba na daga cikin kokarin da rundunar sojin Nijeriya ke yi na rushe cibiyoyin ayyukan masu laifi da kuma ƙara tabbatar da tsaro a Jihar Kogi da sauran jihohin da ke maƙwabtaka da ita.

Rahotanni sun kuma bayyana cewa Battijo shi ne wanda ake zargi da jagorantar hare-hare da dama a yankin, ciki har da harin da aka kai wa cocin Eruku a baya.

By ukarofi

Leave a Reply