An shawarci mahautan Nijeriya su ci gaba da gudanar da sana’arsu cikin tsari

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Wani jigo a ƙungiyar mahautan Nijeriya reshen jihar Legas, Alhaji Ado Garba Bichi, wanda aka fi sani da Ado Garba Araba Aba Kowa, ya shawarci mahautan jihar ta Legas da na Nijeriya baki ɗaya da su ci gaba da gudanar da sana’arsu cikin gaskiya, adalci da bin ƙa’idojin sana’ar fawa.

Alhaji Ado Garba Bichi ya bayar da wannan shawara ne a Legas yayin da yake karɓar baƙuncin wasu gungun mahauta daga babbar mayankar shanu ta Abbatuwa da ke Oko-Oba, Agege, waɗanda suka kai masa ziyarar gaisuwar Sallah tare da yi masa barka da kammala bukukuwan Babbar Sallah lafiya.

Da yake jawabi bayan karɓar baƙinsa, Alhaji Ado Garba ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyara, yana mai cewa hakan alama ce ta haɗin kai da ƙawance tsakanin mambobin ƙungiyar mahauta.

Ya kuma yi musu fatan komawa gidajensu lafiya tare da yi musu nasiha kan muhimmancin sana’ar fawa, wadda ya bayyana a matsayin sana’a mai daraja da mutunci.

A cewarsa, sana’ar fawa tana da matsayi mai girma a tarihin Musulunci, domin wasu daga cikin Annabawan Allah sun gudanar da irin wannan sana’a a rayuwarsu.

“Saboda haka ina ƙara kira ga mahautan Legas da na Nijeriya baki ɗaya da su riƙe wannan sana’a da mutunci da daraja kamar yadda Annabawan Allah suka riƙe ta a zamaninsu,” in ji shi.

Ya kuma buƙaci mahautan jihar Legas da su ƙara haɗa kansu a matsayinsu na mambobin ƙungiya domin su kasance masu magana da murya ɗaya a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Alhaji Ado Garba ya nuna damuwarsa kan ci gaba da hauhawar farashin man fetur da kuma yadda hakan ke ƙara jefa ‘yan Nijeriya cikin matsin rayuwa.

Ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen samar da hanyoyin da za su rage wa al’umma wahalhalun rayuwa tare da inganta walwalar jama’a.

Haka kuma ya bayyana rashin jin daɗinsa kan matsalar tsaro da ke addabar wasu yankunan Arewa, musamman a daidai lokacin da manoma ke fara ayyukan noma a wannan kakar damina.

Ya ce hare-haren ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane na ci gaba da hana manoma gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, lamarin da ka iya shafar samar da abinci a ƙasar nan.

Dangane da haka, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya, gwamnatocin jihohi da shugabannin siyasa masu ruwa da tsaki a Arewa da su haɗa hannu wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro domin bai wa manoma damar gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali.

A ƙarshe, Alhaji Ado Garba Bichi ya yi wa al’ummar Musulmi fatan alheri tare da addu’ar Allah Ya karɓi ibadunsu, Ya kuma ba su damar kammala bukukuwan Sallah cikin zaman lafiya da wadata.

By ukarofi