Tubabbun ‘yan bindiga sun kashe direba da sace mutane a yankin Birnin Gwari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu da ake zargin tubabbun ‘yan bindiga ne a Jihar Kaduna, sun halaka wani direban motar kasuwa tare da yin awon-gaba da wasu mutane tara a hare-hare biyu da suka ƙaddamar akan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Al’amarin ya wakana ne a wani ƙauye da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari a ranar Juma’a.

Haka kuma, an ruwaito cewa direban mai suna Mallam Ibrahim Adamu, jika ne ga ɗaya daga cikin hakiman Masarautar Birnin Gwari.

A cewar wani ɗan gidan su marigayin da ya zanta da ShaharaReporters, an halaka Ibrahim ne a Kwanan Giginya akan babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari a lokacin da maharan suka buɗe wa motar da yake ciki wuta, inda a nan take suka kashe shi tare da yin garkuwa wasu fasinjoji biyar gabanin su tsere.

A wani ɓangare kuwa, an sace wasu manoma guda huɗu yayin da suke tsaka da aiki a gonakinsu a yankin Kurgi da ke Birnin Gwari.

Wannan al’amari ya ƙara haifar da damuwa akan hailn rashin tsaro a yankin Kaduna zuwa Birnin Gwari, wajen da ya jima yana fuskantar matsalolin cin zarafi duk da zaman sulhu a lokuta mabanbanta da ‘yan bindiga.

Mazauna yankin sun bayyana cewa, fitinar tana haddasa cikas ga ayyukan noma, ci-gaban tattali da tsaron ƙauyukansu.

Sun kuma zargi ‘yan bindigar da ke aiki a yankunan nasu da kai hare-hare akai-akai inda su kan ƙwace babura, wayoyin hannu, kuɗaɗe da wasu ababe masu daraja baya ga kashe-kashe da garkuwa da mutane da suke yi.

Akan haka ne suke kira ga ukumomin tsaro da riƙa sintiri a babban titin da ƙarfafa tsaro a ƙauyukan da ke fuskantar matsalolin hare-hare.

By Babaji

Leave a Reply