Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai wani mummunan hari a daren Litinin kan Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabarun Kasa (NIPSS) da ke Kuru, kusa da Jos a Jihar Filato, inda aka kashe jami’an tsaro uku yayin da suke kokarin hana maharan kutsawa cikin cibiyar.
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne da misalin karfe 11:40 na dare, inda suka bude wuta kan jami’an tsaron da ke bakin aiki, lamarin da ya haddasa musayar wuta mai zafi tsakanin bangarorin biyu.
Wani ma’aikacin cibiyar da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa maharan sun kai harin ne ba tare da an yi tsammani ba.
A cewarsa, jami’an tsaro sun yi gumurzu da maharan domin hana su shiga cikin cibiyar, wadda ake kallon ta a matsayin daya daga cikin manyan cibiyoyin tsara manufofin ƙasa a Nijeriya.
Majiyar ta ce jami’an tsaro uku ne suka rasa rayukansu a yayin harin, wadanda suka hada da sojoji biyu da kuma dan sanda daya da ke cikin tawagar tsaron cibiyar.
“’Yan bindigar sun zo ne tsakanin karfe 12 na dare zuwa karfe 1 na dare. Sun karya wani ɓangare na katangar cibiyar sannan suka buɗe wuta kan jami’an tsaro da ke bakin aiki. Sojoji biyu da dan sanda daya sun rasa rayukansu kafin maharan su tsere,” inji majiyar.
Ya ƙara da cewa saurin ɗaukar matakin jami’an tsaro ya hana maharan samun damar shiga cikin cibiyar ko kuma haddasa ƙarin ɓarna.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a gano ainihin manufar harin ba.
Wani mazaunin garin Kuru da ke ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu ya shaida wa jaridar Vanguard cewa mazauna yankunan da ke kusa sun shiga firgici sakamakon ƙarar harbe-harben bindiga da aka riƙa ji na tsawon lokaci a daren.
A lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Jihar Filato ba ta fitar da wata sanarwa kan harin ba, domin ƙoƙarin jin ta bakinta bai yi nasara ba.
Sai dai a wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na NIPSS, Dr. Osime Samuel, ya sanya wa hannu, cibiyar ta tabbatar da aukuwar lamarin tare da bayyana cewa an shawo kan matsalar cikin gaggawa sakamakon martanin jami’an tsaro da sauran hukumomin tsaro.
“An samu nasarar daƙile lamarin cikin sauri sakamakon gaggawar da jami’an tsaro da sauran hukumomin da abin ya shafa suka yi wajen daukar mataki. A halin yanzu babu wata barazana ga lafiyar mahalarta shirye-shirye, ma’aikata, mazauna yankin ko kuma kadarorin cibiyar, kuma harkokin cibiyar na gudana yadda aka tsara,” inji sanarwar.
NIPSS ta ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan harin, tare da jaddada cewa bai dace a fara hasashe kan musabbabin lamarin ko sakamakonsa ba kafin kammala bincike.
Cibiyar ta bayyana cewa tana aiki tare da hukumomin tsaro domin gano hakikanin abin da ya faru, tare da alkawarin sanar da jama’a duk wani sahihin bayani da zarar bincike ya kai ga sakamako.
Haka kuma, Dr. Osime ya yaba wa jami’an tsaron da suka taka rawa wajen dakile harin, yana mai sake jaddada ƙudirin cibiyar na tabbatar da tsaro da lafiyar mahalarta shirye-shiryenta, ma’aikata da mazauna yankin.
