08
May
Rikicin da ke ci gaba tsakanin Hukumar Kula da Kare Haƙƙin Masu Amfani da Kaya ta ƙasa (FCCPC) da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ya jefa kasuwar bashin katin kira da intanet wadda ke da darajar kusan Naira biliyan 400 cikin ruɗani, tare da haddasa cikas ga miliyoyin masu amfani da sadarwa a faɗin ƙsar. Saboda wannan saɓani na doka da iko tsakanin hukumomin biyu, wasu manyan kamfanonin sadarwa sun dakatar da tsarin bayar da rancen katin kira ga abokan hulɗarsu na ɗan lokaci. Wannan mataki ya jefa miliyoyin ‘yan Nijeriya cikin wahala, musamman masu ƙaramin ƙarfi da suka dogara…
