A shekarar 2020, Nijeriya ta rubuta tarihi da ruwan zinariya bayan da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbatar da cewa an kawar da cutar shan inna (wild poliovirus) daga ƙasar gaba ɗaya. Amma shekaru kaɗan bayan haka, wannan nasara mai girma na fuskantar barazana — ba daga ƙwayar cutar kanta ba, sai dai daga ƙin amincewar jama’a da rigakafi sakamakon rashin gaskatawa da yaɗuwar bayanan ƙarya.
ƙididdiga daga bikin Tanar Yaƙi da Cutar Shan Inna ta Duniya na baya-bayan nan sun nuna gagarumin koma baya: sama da gidaje 3,000 a jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara sun ƙi bari a yi wa ’ya’yansu rigakafin shan inna yayin kamfen ɗin rigakafi da aka kammala kwanan nan. Wannan yana nufin dubban yara na fuskatantar barazanar kamuwa da cutar da aka kusan kawar da ita baki ɗaya.
Taken bikin bana — “Kawar da Cutar Shan Inna: Duk Wani Yaro na Buƙatar Rigakafi A Ko Ina Yake” — ya ƙunshi saƙon da ya dace: kowane yaro, kowace allura, ko ina. Domin cutar ba ta bambanta tsakanin yaro ɗan Musulmi ko ɗan Kirista, mai wadata ko talaka — tana buƙatar yaro guda ɗaya da bai samu rigakafi ba domin ta ci gaba da yaɗuwa.
A rahoton Majalisar Tattalin Arzikin ƙasa (NEC), an samu raguwar cutar da kashi 44 cikin ɗari daga shekara ta 2024 zuwa 2025 — daga mutane 109 zuwa 61. Jihohin Kano da Katsina sun samu gagarumar nasara da kashi 89% da 88% na raguwar kamuwa da cutar, amma Sakkwato, Zamfara da Kebbi sun sake fuskantar sabbin masu kamuwa da cutar. Waɗannan ba alƙaluma ne kawai ba — su yara ne da wataƙila ba za su sake tafiya ba saboda rashin samun rigakafi.
Barazanar yanzu ita ce, cVDPV2 (circulating vaccine-derived poliovirus type 2) — wani nau’i ne na ƙwayar da ta samo asali daga allurar rigakafi kanta, wanda ke yaɗuwa idan ba a samu isasshen yawan yara da aka yi wa rigakafi ba.
Matsalar ta fi zama ta rashin amincewa. Duk da cewa gwamnati ta samar da rigakafi, cibiyoyin kiwon lafiya da tsarin sa ido, akwai iyaye da ke rufe ƙofa idan masu rigakafi suka iso. Wasu suna ganin rigakafi da shakku saboda bayanan ƙarya, ra’ayoyin addini da kuma ƙarancin amincewa da gwamnati.
Haka kuma, tsaro da rashin tsafta suna ƙara ta’azzara lamarin. Yin bahaya a fili na gurɓata ruwa, yayin da matsalar tsaro a arewacin ƙasar ke hana masu rigakafi shiga wasu yankuna.
A kamfen na baya, da ya kai yara miliyan 5.3 a jihohin uku, an samu ƙarin yawan wuraren da masu rigakafi suka isa daga kashi 77% a Agusta zuwa 97% a Satumba. Sai dai har yanzu gidaje 3,000 sun ƙi rigakafi — abin da ke nuna cewa tsarin bai isa ba.
A halin yanzu, Kwamitin NEC kan Yaƙi da Shan Inna ya buƙaci jihohi su gaggauta sakin kuɗin da suka ware domin yaƙi da cutar. Amma rahotanni na nuna wasu ba su ɗauki lamarin da muhimmanci ba.
A gaskiya, Nijeriya ba ta buƙatar ƙarin kwamitoci ko rahotanni — tana buƙatar matakan gaggawa guda biyu:
1. ƙarfafa wayar da kai ta al’umma ta hanyar shugabanni na gargajiya da malaman addini su zama manyan jakadun rigakafi.
2. Yaƙi da bayanan ƙarya cikin tsattsauran mataki — kafafen watsa labarai su daina bai wa ƙarya da gaskiya madaidaicin matsayi.
Iyaye da ke ƙin bari a yi wa ’ya’yansu rigakafi ba wai suna kare “’yancin su” ba ne — suna tsoma rayuwar ’ya’yansu cikin haɗari ne. Idan yaro ya kamu da cutar kuma ya yaɗa ta ga wasu, wannan yanki ne na laifin kowa.
Nijeriya ta kashe kuɗi masu yawa tare da goyon bayan WHO, UNICEF, Gavi, da Rotary International wajen kai wannan nasara. Barin ƙalilan daga cikin al’umma su lalata wannan ƙoƙari zai zama abin kunya da asarar shekaru na aiki.
