EFCC ta ayyana neman ɗan China ruwa a jallo bisa zargin damfara

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA, Abuja

Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC), ta ayyana wani ɗan ƙasar China, Peiyuan Niu, a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin karɓar kuɗi ta hanyar yaudara (obtaining money by false pretence).

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Talata, ya ce hukumar na neman taimakon jama’a domin gano inda mutumin yake.

Sanarwar ta bayyana cewa Peiyuan Niu mai shekaru 40 ɗan ƙasar China ne, kuma adireshinsa na ƙarshe da aka sani shi ne lamba 111, Kudirat Abiola Way, Oregun, a Jihar Legas.

Sanarwar ta ce: “Ana sanar da jama’a cewa Peiyuan Niu, wanda hotonsa ya bayyana a sama, Hukumar EFCC na nemansa ruwa a jallo bisa zargin karɓar kuɗi ta hanyar yaudara.”

Hukumar ta buƙaci duk wanda yake da wani bayani da zai taimaka wajen gano inda mutumin yake da ya tuntuɓi ofisoshinta da ke Ibadan, Uyo, Sokoto, Maiduguri, Benin, Makurdi, Kaduna, Ilorin, Enugu, Kano, Legas, Gombe, Fatakwal ko Abuja.

Haka kuma ana iya tuntuɓar hukumar ta hanyar lambar waya 08093322644, ko kuma ta adireshin imel: [email protected]ɓ.ng, ko kuma a sanar da ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko sauran hukumomin tsaro.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake zargin wani ɗan ƙasar China da aikata zamba a Nijeriya ba.

A watan Disambar shekarar 2024, EFCC ta kama mutane 792 a Legas a wani samame mafi girma da ta ta a kaiwa kan masu aikata damfara ta intanet da zamba ta soyayya (romance scam).

Rahotanni sun nuna cewa daga cikin waɗanda aka kama a lokacin akwai ‘yan ƙasar China 114, Filipinos 40, ‘yan Kazakhstan biyu, ɗan Pakistan guda ɗaya da kuma ɗan ƙasar Indonesia guda ɗaya.

Wasu daga cikin waɗanda aka kama a wancan lokaci an riga an yanke musu hukunci bisa laifukan damfara ta intanet.

By ukarofi