Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Haƙiƙa harshen Hausa na daga manyan harsuna a duniya kuma ya yaɗu don yadda ya kan ari kalmomi daga wasu harsuna ya maida su Hausa. Harsunan da Hausa ya fi ɗaukar kalmomin sa shi ne Larabaci don alaƙar addinin Musulunci. Na biyu sai harshen Turancin inigilishi don zuwan Turawan mulkin mallaka. Harshen Hausa ya aro wasu kalmomin daga wasu ƙananan harsuna ko ma manya na Afirka da hakan ya ƙara ba shi tagomashin bunƙasa. Lamuran fatauci sun kai Hausawa wasu ƙasashe kamar Ghana inda harshen Hausa ya yadu a can amma ya samu tasirin sauya salon furuci don cuɗanya da wasu harsunan ƙasar. Masu tafiya gabar ko ƙasar Makkah don aikin hajji sun yaɗa zango a ƙasashe da su ka haɗa da Chadi da Sudan har su ka kafa anguwannin Hausawa ko Hausawi. Idan ka shiga Makkah da Madina za ka samu jikokin Hausawa da a ka haifi iyaye da kakannin su a can na magana da harshen Hausa amma da tasirin Larabci. Za ka ji yaro Bahaushe na cewa abokin wasan sa “zan nazzalo ka” wato zai ingizo shi daga wa imma saman bene ko wani tudu. Ko babban mutum ya zaiyana wani ɗan uwan zaman sa da cewa “wannan sahibi ai manzil ɗin mu ɗaya ne” wato ma’ana wannan abokin na wa gidan mu ɗaya ne. Masu sayarda kaya a Makkah, Madina da Jiddah kan yi ƙoƙarin magana da harshen Hausa don yadda Hauwasa ko masu magana da Hausa kan zama kan gaba wajen sayen kayan tsarabar Makkah da Hausawa ke zayyanawa da “kayan gabar”. Mutan ƙasar Sin na ƙoƙarin koyon Hausa ba tare da samun cuɗanya mai ƙarfi da Hausawa ba don haka sai harshen su na gado ke tasiri ainun a yadda su ke furta kalmomin Hausa. Na je birnin Kaulaha a ƙasar Senegal na samu hausawa a can da waɗanda su ka koyi Hausa a sanadiyyar tafiya can don hulɗa da Shehun ɗarikar Tijjaniyya Ibrahim Niasse wanda ɗan ƙabilar Walop ne. Akwai binciken da na gani da ba ni da tabbacin sahihancin sa da ke nuna harshen Hausa shi ne na 11 mafi tasiri ko bunƙasa a duniya. Ko binciken ba shi da sahihanci to a gaskiya ba zai zama nesa da gaskiyar ba in ka duba manyan harsunan duniya kama daga Larabci, turancin Ingilishi, Turancin Faranshi, Sifaniyanci, Bengali, Indunusiyanci, Sinanci, Indiyanci, Rashanci, Swahili da Amharic to haƙiƙa za a ba wa harshen Hausa gurbi. Ko da dai harshen turancin Ingilishi a ke amfani da shi a Majalisar ɗinkin Duniya, cikin ikon Allah a haramin Makkah a kan yi amfani da harshen Hausa wajen ishara ko nuna alamun wajaje, kazalika ya na daga harsunan duniya da a ke amfani da su wajen fassara huɗubar Juma’a ko ta idi don amfanin miliyoyin masu amfani da harshen. Na ziyarci jagoran masu fassara da harshen Hausa na haramin Makkah Sheikh Abdulrahman Sani Yakub a ofishin sa a jikin babban masallacin na harami. Abun da na gani ya kayatar da ni don Hausa na da sashe na musamman da ma’aikata masu hazaƙar gaske da a ke girmamawa. Akwai manyan jami’o’i na duniya da ke da tsangayar nazarin harshen Hausa. Ba mamaki bunƙasar harshen da zaman sa ɗaya daga masu tasiri a duniya ya sa ya wuce matsayin na wani gida ko wani mutum ko wata ƙungiya. In mun duba akwai Balarabe amma harshen Larabci a wajen Musulmi na Alkur’ani ne kamar yadda Allah madaukakin Sarki ya ambata ko a nan kusa cikin izu 10 suratul ahkaf aya ta 12. Ga suratu Yusuf aya ta 2 duk na magana da saukar da Alkur’ani da harshen Larabci. Malamai ma na bayanin harshen Larabci shi ne harshen ‘yan aljannah kuma ba na tsammanin Larabawa ne kaɗai ko masu magana da harshen Larabci kaɗai za su shiga aljannah. Balarabe ka iya bugar kirji ya ce shi Balarabe ne amma mallakar harshen Larabci ya fi ƙarfin sa. Su ma Turawa kan yi alfahari da wanda ya ke jin harshen su don samun saukin hulɗa da shi kuma sai dai su nunawa baƙaƙen fata babban launi kamar yanda ya taɓa aukuwa a Afurka ta kudu amma ba su isa su haramta ma sa amfani da tinƙaho da magana da Turanci ba. Duk wadannan harsunan za a iya yin taro don bunƙasa su ko yin gasa kan kwarewa wajen amfani da su amma ba a ware rana ta musamman a ce yau ranar Turawa ko Larabawa ce ta duniya da sauran su. Ma’ana girman harsunan ya fi gaban gaban ma’abotan sa su ware rana don ƙabilar su sai dai don tasirin harshen da hakan ma ba lallai masu shirya taron su zama ‘yan asalin harshen ba. Bakaken fata a nan Abuja sun gaiyace ni taron kwarewa wajen rubuta ƙasida ko waƙa da harshen Larabci kuma har ga Allah sun yi magana da Larabci kamar ruwan sama!
Na ga an yi taron harshen Hausa a ƙasar Ghana inda a ka duba tasirin harshen Hausa kan wasu harsuna na ƙasar. A tarihi Hausawa sun shiga Ghana ne don fataucin goro don albarkar da Allah ya yi wa ƙasar da goro da ‘yan kasuwar goro ke kira da “dan Ankara”. Ba zan wuce wannan gabar ba sai na yaba wa al’ummar jamhuriyar Nijar da ke da harsuna daban-daban ciki kuwa da harshen Hausa. Yabon ya shafi yanda za ka taras ɗan Nijar na iya magana da aƙalla harsuna uku zuwa hudu na ƙasar ta sa. Bahaushe na iya magana da Zabarmanci, Tamasheƙ, Fulfulde da kuma Faransanci da hakan don yadda ƙasar Faransa ta yi wa Nijar ɗin mulkin mallaka. Kar ka yi mamaki ka samu Bahaushe a Kano, Daura ko Zazzau ba ya iya magana da kowane harshe waje da Hausa. Kazalika wanda Hausar sa ma ta yi tsanani ko makarantar book ya shiga ba zai iya koyon harshen Turanci ya yi magana da shi ba inda-inda ba. Wannan ‘yar gazawar ta wasu daga Hausawa na buƙatar faɗakarwa don samun canji ko gyara don gyara kayan ka bai zama sauke mu raba ba.
Harshen Hausa abun alfahari ne ga miliyoyin mutane musamman a Afurka ta yamma da wasu sassan duniya. Harshen ya zama na mu’amalar kasuwanci, diflomasiyya da addini. Haƙiƙa akasarin wadanda su ka yiwa harshen hidima ta hanyar rubutun zube Turawa ne. Mu duba yadda Bature RM East ya bukaci marigayi Abubakar Imam ya rubuta “Magana jari ce” na 1-3. Mu duba yanda Jean Boyd ta rubuta shaharerren kamus na Turanci zuwa Hausa. Gudunmawar wasu Turawan wajen raya harshen Hausa ba karama ba ce a fannin sadarwar rediyo in mu ka duba Barry Burgess a London, Steɓe Lucas a Washington, Thomas Mosch a Jamus. Don haka harshen na duniya ne da wadanda ba asalin masu harshen ba su ka bada gagarumar gudunmawa wajen bunkasa shi har ya kai matsayin shaharar da ya ke da ita a yau. Abun da ya ban takaici na yi wannan rubutun shi ne yadda wasu ke yada kamfen ɗin nuna kyama ga waɗanda su ka share shekaru aru-aru su na hidima ga harshen. Kazalika wasu ma da ke yaɗa wannan kamfen ɗin ba ma Hausawa ba ne kamar yadda su ke ikirari a kafafe masu arahar yaɗa ra’ayi na soshiyal midiya. Na ga wani ma daga Gobir na kushe Sarkin Daura da cewa ba Bahause ba ne. Wasu na cin zarafin wani ɗan jarida da ya ba da gudunmawa ga bukin ranar Hausa don wai ba Bahaushe ba ne! don haka ya haramta ya halarci taron Hausa. Masu biyewa irin wannan kamfen ɗin da tunanin ko masu kishin Hausawa ne su k eke yaɗa fitinar, za ka tarar wa imma yara ne kanana da ba a dade da yaye su ba ko kuma makiya haɗin kan yankin arewa ne da ke neman damar wargaza yankin. Na tabbata in wannan kiyaiya da a ke gani kamar kishi ne ta haɓaka duk girman arewa ba za ta zaunu ga kowa ba. In za ka ba da ra’ayi ka duba jama’ar da ka ke rayuwa a cikin su daga makwabtan ka zuwa limamin anguwar ku da waɗanda ku ke sana’a tare ko ku ka yi makaranta tare, za ka ga harshen Hausa ko addini ya hada ku amma ba lallai ƙabilar ku ta asali ɗaya ba ce. Hakanan in ka kara nazari za ka tuna abun alheri da wani wanda ba ku haɗa addini ko ƙabila ɗaya ba ya yi ma ka da wanda ƙila ku ka fito gida ɗaya bai yi ma ka ba don kasancewar ku ‘yan uba ko wata ƙiyayya ta daban ta ɓata dangantakar ku.
KAMMALAWA
Ya zama mai muhimmanci masu yaɗa mummunan kamfen na haddasa ƙiyayya tsakanin Hausawa da Fulani su sani cewa ba kowa ba ne gafalalle ba zai biye mu su. Gaskiya ne akwai Hausawa kuma akwai Fulani ko a ce akwai harshen Hausa da Fullanci. Abun da a ke nufi da Hausa/Fulani shi ne yadda ƙabilun biyu ke haɗe ta hanyar addini da auratayya. Zaman waɗannan ƙabilu biyu tare ya ba wa yankin arewacin Nijeriya ƙarfin da ya hana masu yunƙurin shigar da fitina yankin nasara. Duk mai kuɗin goro ya ce Fulani ‘yan ta’adda ne don samun ɓarayin daji da Fulani a ciki sam bai yi adalci ba. Kakaf masu ta’addancin nan ba su kai kasha ɗaya cikin 100 na yawan Fulani ba. Idan ‘yan tsiraru a kabila sun zama mugaye ba adalci ba ne wani ya tsaya kai da fata sai ya yi ɓatanci ko sharri ga dukkan ‘yan wannan ƙabilar. Na ga wani shafi a yanar gizo ya saka wani mai kamar Fulani makiyayi na umurtar shanun sa su cinye amfanin wata gona. Ban tantance ko faifan na fasahar AI ba ne ko kuwa gaskiya ne. Na tambayi masu shafin irin waɗannan tambayoyin: shin dukkan Fulani makiyaya ne na shanu? Shin dukkan Hausawa manoma ne? shin ba manoma a cikin Fulani? Kasha nawa ne cikin 100 na Fulani ke aikata ta’addanci? Na buƙaci amsa a jaridance ba ra’ayi ba. Ma’abota shafin sai su ka maimaita rubuta suna na su ka saka alamar dariya!
