Za mu daɗe muna yabon auren ƙabilu muna kushe namu

Spread the love

Daga UNCLE LARABI

Mata sun fi son a yi musu ƙarya, ko na kalamai ne, a neman aure, amma idan an yi aure cefane da neman abinci ba zai bayar da damar wannan yin ƙaryar ba tunda komai na zahiri ya gama bayyana. To, shi ya sa ake shan wahalar zamantakewa a gidajen Bahaushe na aure, saboda ba ma amfani da zahiri da gaskiya wajen neman auren. Mun fi son ƙarya da burgewa.

Za mu daɗe muna cewa auren wasu ƙabilun yafi ƙarko. Misali; idan ku ka ɗauki ƙabilar Edo, Musulmai, ba Kirista ba, idan namiji zai yi aure sai macen ta zo gidansu wajen mahaifiyarsa ta zauna tsahon wata uku ko shida. Idan uwar ta mutu, za ta zauna a wajen babbar yayarsa ko wajen wata babba a danginsu. A wannan zaman, ba abin da zai haɗa ta da mijin na iskanci ko kwana waje ɗaya, don na san wasu za su yi zargin hakan. 

Kawai abinda ake so shine, a ga halayenta da nagartarta da juriyarta. Idan ta ci wannan Jarrabawar sai jarrabawa ta gaba ita ce, ranar da aka yi auren ba a fara kai ta gidan miji wajen babarsa ko wata babba a dangi, idan uwar ta mutu ake yi. Sai ta sake yin sati ɗaya ko biyu a gidan. Dangin mijin sai su mai masa ita ɗakinsa idan an gama hakan. 

Shin mu Hausa-Fulani haka muke Yi? Akan kayan lefe ko gida ko yin ‘party’ ko wani abu ƙanƙani sai a fasa biki. Su kuwa ƙabilun duk wannan ba ya gabansu. 

Wallahi na san auren da aka fasa akan kayan lefe. Wai ya kai sun yi kaɗan kuma sun yi ƙanana ya je ya canjo. Mijin ya ce, tunda shi za ta sawa, shi su yake so ta saka, ba zai canja ba. A haka auren ya lalace ba a yi ba.

Na ga auren da uban yarinyar ya ce, ɗaurin aure ranar Lahadi yake so a yi, uban yaro da shi suka ce Juma’a suke so. ƙarshe an fasa auren. Wallahi waɗannan makusanta ne ma sosai na zamantakewar unguwa, na san iyayen sama da shekaru 30. To, a haka muke so mu ga daidai a gidajen auren namu?

Wata matar Bahaushe akan ashana ko gishiri ko magi ko naman miya, sai a yi rigima har da sakin aure. Haka matan ƙabilun suke yi? Don Allah wa zai iya ba ni labarin ya taɓa ganin an je ganin kayan lefenta wata ƙabilar a unguwarsu?

Uncle Larabi, wanda cikakken sunansa shine, Abdullahi Jibril Larabi, marubuci ne a Kano. Za a iya samun sa a 08065418892

Alhamis, 16 ga Afrilu, 2026

By ukarofi