Daga ALI ABUBAKAR SADIƙ
Kimanin sati biyu da suka gabata na yi wani rubutu mai taken “Manaƙisar Amurka Ga Arewa.” Abubuwa biyu ne suka faru a wancan lokaci.
Na farko shine, sanarwar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran. Na biyu kuma shine, bayanin ƙasar Amurka na umarta ma’aikatan jakadanci da ’yan ƙasarta su bar Nijeriya da kuma nesantar jihohin Arewa.
Kamar yadda na bayyana a wancan rubutu cewa, tunda Iran ta gagari Amurka, inda ta kasa cimma muradinta da kuma datse mashigin Hormuz da Iran ta yi, wanda ya janyo tashin gwauron zabi na farashin mai a duniya, yanzu Nijeriya ce a taswirar inda Amurkan ta dosa.
Ajandar gwamnatin Trump ita ce, ƙoƙarin mamaya da mallakar wani iko a ƙasashe uku masu mafi yawan mai a ƙarƙashin ƙasa da ke nahiyoyin Amurka ta Kudu (ɓenezuela) Gabas ta tsakiya (Iran) da Afirka (Nijeriya).
Sun riga sun mamaye ɓenezuela, sun gwada Iran abin bai kasance yadda suka tsara ba. Yanzu hankalinsu ya karkato kan Nijeriya.
Idan ba mu manta ba, wasu masu dattin ƙabilanci da bambancin addini aka yi amfani da su ba su sani ba, suka iza wutar maganar cewa, ana yi wa Kiristoci kisan ƙare-dangi a Arewa; bin da ya bai wa Amurka ƙofar da take nema.
A ranar Kirsimeti suka kawo hari Nijeriya a Sokoto, ba yankin Kaduna (Birnin Gwari) ko Katsina da Zamfara ba, inda ake da sansanonin ’yan ta’addan daji da ke cin karensu babu babbaka ba. Sannan suka turo sojoji ’yan leƙen asiri (kimanin 200), waɗanda aka kai Bauchi (ba Katsina ko Zamfara ba). A cikin waɗannan watanni, waɗannan sojojin na Amurka, na san cewa zuwa yanzu sun gama nazarin (mapping) Arewacin Nijeriya gabaɗaya da ‘reeper drones’ ɗinsu, wato jirgi maras matuƙi.
To, a jiya kuma sai ga Ted Cruz a wani bidiyo ya bayyana a gaban kwamitin harkokin waje na majalisar dattawan Amurka, inda yake sake jaddada maganar kisan ƙare-dangi kan Kiristoci, har da bayanin cewa, a duniya babu inda ake kashe Kiristoci kamar Nijeriya, domin an hallaka sama da 50,000 tare da ƙone majami’u da makarantu na Kiristoci sama da 20,000.
Ted Cruz, ɗin nan sune ’yan gaba-gaba wajen ingiza Trump ya biye wa Israila wajen far wa Iran da farmaki. Iran ba irinmu ba ce, ta tashi ta kare kanta, saboda su na da shugabancin da al’umma ce a gabansu.
’Yan siyasarmu babu abinda ke gabansu illa kawai ta yaya za su ci zaɓe, domin su ci gaba da wadaƙa da kuɗaɗenmu. Babu lokaci mai haɗari a Nijeriya irin lokacin da aka doso zaɓe da lokacin yin sa. Muna barci da sakarci da tsanar juna da iza wutar ƙabilanci da ɓangarancin addini, a na can a na ƙoƙarin tarwatsa mu.
Mu sani wallahi babu abinda muka fi Libya, Iraƙ, Sudan, Syria da Yemen… Yau su na ina? Duk an tarwatsa su! Tun bayan kifar da Ghaddafi Amurka ta ɗana mana tarko da zaton za mu faɗa a 2015, har su ka bugi ƙirjin cewa, Nijeriya za ta tarwatse a 2015. Allah ya ƙwato mu, amma ’yan siyasa na daɗa nutsar da mu.
Shin hasashen da Amurka ta gaza samarwa a shekarar 2015 shine ta ke son ya afku a 2027? To, mu sani, sai mun bayar da dama haƙarsu za ta cimma ruwa. Shin za mu tsaga wa ƙadangare bangon da zai sami shiga ne ko kuwa?
Malam Ali Abubakar manazarci ne a birnin Kano
