An kashe ɓarawo ɗaya bayan kashe Daraktan Mulki a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Al’ummar garin Yauri da ke jihar Kebbi sun wayi gari cikin ruɗani bisa kisan Alhaji Nasiru Muhammed, wanda shine Daraktan Mulki da Gudanarwa (DPM) a ƙaramar hukumar Ngaski da ke jihar.
Alhaji Ahmed, Sarkin Yaƙi Yauri, ya bayyana cewa, ‘yan bindiga sun shiga gidan Alhaji Nasiru da misalin ƙarfe 2:00 na daren Juma’a a unguwar Low Cost da ke garin Yauri, inda suka yi gaba da iyalansa da waɗansu mata daga gidajen da ke maƙotaka da shi bayan sun kashe shi sanadiyyar dagewsrsa ta cewa ba zai bi su ba.
Ya ƙara da cewa, an sami gawar Marigayi Alhaji Nasiru ne a bayan gidansa.
Ya ce, an tabbatar da sun ɗauki mai ɗakinsa, Rukayyatu Abdullahi
da ƙarin mata biyu ciki har da wata Malama Maryam Salihu da ke koyarwa a makarantar Abarshi Secondary School a Yauri.
Sai dai jami’an tsaro sun sami nasarar kashe ɗaya daga cikin ɓarayin tare da samun motar da ɓarayin suka yi amfani da ita a lokacin kai farmakin.

By ukarofi

Leave a Reply