NiMet ta yi hasashen mamakon ruwan sama na kwana uku daga Asabar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da Yanayi ta Ƙasa NiMet, ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama da hasken rana daga ranar Asabar zuwa Litinin a sassan Nijeriya.

A takardar bayanin hasashen da ta fitar a ranar Juma’a a Abuja, NiMet ta ce rana za ta haska a yankin arewacin Nijeriya da kuma matsakaicin hadari.

Hukumar ta yi hasashen samun tsawa da walƙiya da matsakaici ruwan sama a wasu sassan jihar Taraba a lokutan rana da kuma dare.

Ta ce, za a samu yanayin hadari a Arewa ta Tsakiya a tsakanin ranakun a sassan ƙasar.

A kudancin ƙasar, jihohin Ondo, Osun, Ogun, Lagos, Imo, Abia, Enugu, Ebonyi, Anambra, Cross River, Akwa Ibom, Rivers, Bayelsa, Edo da Delta za su fuskanci hadari mai tsawa a rana da kuma dare.

NiMet ta bayyana cewa, hukumar ta ce za a yi hadari da kuma samun hasken rana lokaci bayan lokaci da matsakaici ruwan sama a jihohin Delta, Edo, Bayelsa, Kuros Riba, Akwa Ibom da Ribas a yammaci.

A cewar hukumar, za a samu sauye-sauyen yanayi mai tsanani da ka iya haifar da takura, don haka ta kirayi al’umma da su ɗauki matakan kariya wajen sanya kayan sanyi a jikinsu da zama a wurare masu matsakaicin yanayi.

By Babaji

Leave a Reply