Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Sufurin Jiragen Sama da Raya Harkokin Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya bayyana cewa Nijeriya ce ke da mafi yawan jiragen sama masu zaman kansu a nahiyar Afirka, yana mai cewa bunƙasar wannan fanni ta buɗe babbar dama ga ƙasar wajen jawo sabbin masu zuba hannun jari da ƙarfafa haɗin gwiwa da manyan kamfanonin ƙera jiragen sama na duniya.
Keyamo ya bayyana hakan ne a birnin Montreal na ƙasar Kanada, yayin wata ganawa da kamfanin Bombardier, bayan kammala ziyarar aiki da ya kai cibiyar kammala ƙera jiragen saman kamfanin mai suna Laurent Beaudoin Completion Centre.
A cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Ministan Shawara na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa, Tunde Moshood, ya fitar, an ce wannan ziyara ta kasance ƙarshen jerin ganawa da manyan kamfanoni huɗu da suka fi shahara wajen ƙera jiragen sama a duniya, wato Boeing, Airbus, Embraer da Bombardier.
Sanarwar ta ce, an gudanar da ganawar ne domin samar wa kamfanonin jiragen saman Nijeriya damar samun sabbin jiragen sama, hanyoyin samun tallafin kuɗi, goyon bayan fasaha da sauran shirye-shiryen da za su inganta harkokin sufurin jiragen sama a ƙasar.
Keyamo ya ce kasuwar jiragen sama masu zaman kansu na ci gaba da bunƙasa a Nijeriya, lamarin da ya sanya ƙasar cikin manyan kasuwannin sufurin jiragen sama a Afirka. Ya ƙara da cewa, yawan jiragen sama masu zaman kansu da ke aiki a Nijeriya wata babbar dama ce da za a yi amfani da ita wajen haɓaka harkokin sufurin jiragen sama.
“Nijeriya ce ke da mafi yawan jiragen sama masu zaman kansu a Afirka. Wannan babbar kasuwa ce, kuma muna son amfani da wannan ƙarfi wajen gina alaƙa mai ƙarfi da kamfanonin ƙera jiragen sama, samar da damammaki ga masu gudanar da harkokin jiragen sama da kuma bunƙasa masana’antar sufurin jiragen sama ta ƙasar,” inji shi.
Ministan ya bayyana cewa babbar manufar Gwamnatin Tarayya ita ce haɗa masu gudanar da jiragen sama na cikin gida kai tsaye da manyan kamfanonin ƙera jiragen sama domin sauƙaƙa sabunta jiragensu tare da inganta ƙa’idojin aiki a masana’antar.
A cewarsa, ƙarfafa haɗin gwiwa da waɗannan kamfanoni zai taimaka wa kamfanonin jiragen saman Nijeriya wajen sabunta jiragensu, ƙara matakan tsaro, inganta ingancin aiki da kuma tabbatar da ɗorewar fannin sufurin jiragen sama na ƙasar.
“Tun farko manufarmu ita ce haɗa masu gudanar da jiragen sama na Nijeriya kai tsaye da manyan kamfanonin ƙera jiragen sama domin ƙarfafa ƙwarewar cikin gida, sabunta jirage, inganta tsaro da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a wannan fanni,” inji Keyamo.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da aiwatar da sauye-sauye da za su ƙarfafa zuba jari a fannin sufurin jiragen sama tare da samar da yanayi mai kyau ga kamfanonin jiragen sama da sauran masu ruwa da tsaki. Tawagar Najeriya ta haɗa da Babban Daraktan Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA), Kyaftin Chris Najomo; Manajan Darakta na Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Tarayya (FAAN), Olubunmi Kuku; Wakilin Nijeriya a Majalisar Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (ICAO), Injiniya Mahmoud Sani Ben-Tukur, tare da sauran jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki a fannin sufurin jiragen sama.
Yayin ziyarar, tawagar ta zagaya sassan ƙera jiragen sama da cibiyoyin kammala aikin jiragen Bombardier, inda aka yi musu bayani kan tsarin kula da jirage, horas da matuƙa da injiniyoyi, fasahar zamani a harkokin jiragen sama, ayyukan gyara da kula da jirage, da hanyoyin mallakar jiragen sama.
Kamfanin Bombardier na daga cikin manyan kamfanonin duniya da ke aera jiragen sama masu zaman kansu, inda yake ƙera nau’ikan jiragen Challenger da Global, tare da ba da sabis na gyara, horaswa da tallafin fasaha.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa wannan haɗin gwiwa zai buɗe sabbin damammaki a fannoni da suka haɗa da sabunta jiragen sama, ayyukan Gyara da Kula da Jirage (MRO), tallafin injiniya, horaswa, bunƙasa ƙwarewar fasaha da musayar fasahar sararin samaniya. Ta kuma ce wannan mataki ya yi daidai da sauye-sauyen da ake aiwatarwa domin ƙarfafa masu gudanar da jiragen sama a Nijeriya su mallaki sabbin jirage masu aminci da rage amfani da makamashi, tare da ƙarfafa alaƙa da kamfanonin ƙera jiragen sama, masu ba da kuɗaɗen tallafi da masu ba da jirage haya.
A cewar gwamnati, ganawar da aka yi da kamfanonin Boeing, Airbus, Embraer da Bombardier na nuna ƙudirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na mayar da Nijeriya cibiyar harkokin sufurin jiragen sama ta farko a Afirka ta hanyar haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa, haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu da kuma sauye-sauye masu ɗorewa.
