Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An bayyana cewa Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Amfani a Fannin Lafiya ta Jihar Kano (Drugs and Medical Consumables Supply Agency – DMCSA) na ci gaba da samar wa Asibitin Abubakar Imam Urology Centre magunguna da kayan aikin tiyata masu inganci ta hanyar tsarin Drug Revolving Fund.
A ƙarƙashin wannan tsari, ana sayar wa marasa lafiya magunguna a farashi mai sauƙi, sannan kuɗaɗen da aka samu daga sayar da su ake amfani da su wajen sake sayo sabbin magunguna domin tabbatar da wadatarsu a kowane lokaci.
Shugaban Asibitin Abubakar Imam Urology Centre, Dakta Balarabe Umar Muhammad, ne ya bayyana hakan, inda ya ce asibitin ya samu ci gaba sosai saboda dukkan magungunan da suke buƙata suna samunsu daga DMCSA cikin sauƙi da araha.
Ya ce irin wannan tsari ne ake aiwatarwa a mafi yawan asibitocin gwamnati na jihar Kano, tare da yaba wa hukumar bisa samar da magunguna da kayan aiki masu inganci waɗanda Hukumar NAFDAC ta amince da su.
Dakta Balarabe ya bayyana hakan a matsayin wata babbar nasara ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Darakta Janar na DMCSA, Pharmacist Ghali Sule, saboda ƙoƙarinsu na tabbatar da samar da ingantattun magunguna da rarraba su ga asibitocin gwamnati a faɗin jihar.
Ya ƙara da cewa DMCSA na ƙarƙashin jagorancin ƙwararren masanin hada magunguna, Pharmacist Ghali Sule, wanda ya ce yana gudanar da aikinsa cikin gaskiya da jajircewa.
Dangane da ci gaban da aka samu a asibitin, Dakta Balarabe ya ce tun bayan hawansa muƙamin Babban Daraktan Asibitin (CMD), an samu gagarumin sauyi sakamakon goyon bayan gwamnatin jihar da kuma Ma’aikatar Lafiya.
Ya bayyana cewa an samar wa asibitin sabbin kayan aiki da suka haɗa da na’urar Digital ɗ-ray Machine da aka saya kan sama da Naira miliyan 74, tare da batura da na’urorin inverter domin tabbatar da samar da wutar lantarki ba tare da katsewa ba.
Hakazalika, an samar da na’urar Ultrasound Machine mai darajar sama da Naira miliyan 40, yayin da gwamnatin jihar ta kuma samar da tsarin hasken rana (Solar Power System) a sassan marasa lafiya, sashen wanke koda (Dialysis), sashen gaggawa (Emergency) da kuma sashen kula da marasa lafiya na waje (OPD), kan kuɗi sama da Naira miliyan 57.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta yi alƙawarin faɗaɗa tsarin hasken rana zuwa sassan Pharmacy, Laboratory, ɗ-ray da kuma ginin gudanarwa kafin ƙarshen shekarar 2026.
Dakta Balarabe ya bayyana cewa an samu aiwatar da waɗannan ayyuka ne ta hannun Hukumar Kano State Healthcare Eƙuipment and Facilities Trust Fund (KHETFUND), wadda ke karɓar buƙatun asibitoci tare da aiwatar da su bayan amincewar gwamnatin jihar.
A ƙarshe, ya yaba wa Shugabar KHETFUND, Dakta Fatima Usman Zaharaddeen, bisa irin jajircewa da goyon bayan da take bai wa Asibitin Abubakar Imam Urology Centre da sauran asibitocin gwamnatin jihar Kano.
