Mun samu kyakkyawar tarbiyya daga wajen iyayenmu — Dakta Balaraba Ganduje

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Daya daga cikin ‘ya’yan tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wato Hajiya Dakta Balaraba Abdullahi Umar Ganduje, ta bayyana cewa tana da ƙwarin gwiwar ci gaba da janyo da tallafa wa matasa masu karatu da masu sana’a, har ma tana ɗaukar wasu daga cikinsu a matsayin ‘yan kafafen sada zumunta na ƙungiyarta.

Hajiya Balaraba ta ce duk wanda zai ce shi ɗan social media ne na Balaraba amma ba shi da aiki ko kuma baya zuwa makaranta, to daga yanzu sun rabu.

“Abin da na ga ya fi ga wasu ‘yan media shi ne su je su nemi sana’a. Ni gara in san kana da sana’a ina taimaka maka. Muradina shi ne kowa ya zama yana aiki, ko yana makaranta, ko yana da wani abu na dogaro da kai. Siyasa sai da sana’a, domin dukkanmu sana’a muke yi,” inji ta.

Hajiya Balaraba ta ƙara da cewa abin da suka koya daga iyayensu shi ne taimakon al’umma da jajircewa ba tare da gajiyawa ba.

“Yau za mu yi taimako, gobe za mu yi, idan an sake nema washe gari ma za

By ukarofi

Leave a Reply