Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Jihar Neja ta hana makarantu masu zaman kansu gudanar da bukukuwan yaye dalibai, tare da umartar dukkan cibiyoyin ilimi masu zaman kansu da su maye gurbinsu da bukukuwan gabatar da jawabi da bayar da kyaututtuka domin karrama nasarorin ɗalibai.
News Point Nigeria ta ruwaito cewa an ƙaddamar da wannan tsari ne ta hannun Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu ta Jihar Neja, domin daidaita shirye-shiryen ƙarshen zangon karatu da kuma magance abin da hukumomi suka bayyana a matsayin yawaitar bukukuwan yaye dalibai masu tsada da nuna almubazzaranci a makarantu masu zaman kansu.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Ayyukan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta jihar, Yunusa Ibrahim, ya fitar, gwamnatin ta ce makarantu su riƙa amfani da bukukuwan gabatar da jawabi da bayar da kyaututtuka wajen karrama ɗalibai saboda ƙwazo a karatu, kyawawan ɗabi’u, nagartaccen jagoranci da sauran fitattun nasarori.
Sanarwar ta bayyana cewa yadda ake gudanar da bukukuwan yaye dalibai cikin tsada da nuna alfarma ya jefa iyaye cikin nauyin kuɗaɗe da ba dole ba, tare da haifar da gasa mara kyau tsakanin makarantu.
Gwamnatin ta kuma lura cewa da dama daga cikin waɗannan bukukuwa sun kauce daga ainihin manufarsu ta ilimi, inda kashe kuɗaɗe da manufofin kasuwanci suka mamaye bikin murnar nasarorin ilimi.
Ta ce sabon umarnin na da nufin dawo da matsakaici, ƙarfafa tarbiyya da kuma tabbatar da cewa shirye-shiryen ƙarshen zangon karatu sun ci gaba da mayar da hankali kan sakamakon ilimi da ƙwarewar ɗalibai.
Domin tabbatar da bin wannan umarni, Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu ta Jihar Neja, tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai da sauran masu ruwa da tsaki, za su gudanar da yaƙin wayar da kai a faɗin jihar domin ilmantar da makarantu da jama’a game da sabon tsarin.
Haka kuma, an ɗora wa jami’an yaɗa labarai da masu wayar da kan al’umma alhakin tattaunawa da shugabannin makarantu, iyaye da al’ummomi domin tabbatar da fahimta da aiwatar da wannan umarni.
Gwamnatin jihar ta sake jaddada aniyarta na inganta matsayin ilimi da kare muradun ɗalibai da iyaye, tana mai cewa dole ne ayyukan makarantu su kasance cikin ƙa’idojin ilimi da aka amince da su da kuma kyawawan hanyoyin gudanarwa.
Ta kuma yi kira ga makarantu, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki da su mara wa wannan shiri baya, tana mai bayyana shi a matsayin wani mataki na inganta tarbiyya, daidaito da kuma ƙwazon ilimi a faɗin jihar.
